Ba cin amanar kasa jagoran 'yan adawar Zambia ya yi ba —Amnesty

Da ma dai Hichilema na fuskantar tuhume-tuhume a kan tunzura jama'a su yi bore tun a watan Oktoban bara
Image caption Da ma dai Hichilema na fuskantar tuhume-tuhume a kan tunzura jama'a su yi bore tun a watan Oktoban bara

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bayyana tuhumar cin amanar kasar da ake yiwa jagoran 'yan adawa a Zambia da kuma wasu mutane biyar a matsayin gallazawa, in da ta yi kira a kan ayi watsi da tuhumar.

An kama Hakainde Hichilema ne bayan ya tarewa kwambar motocin shugaban kasa Edgar Lungu hanya.

Hayaniya ta ɓarke a lokacin da kwambar motocin shugaban ta yi ƙoƙarin shige na Hichilema.

'Yan sanda sun ce kwambar motocin Hakainde Hichilema ta sanya rayuwar shugaban kasar cikin hadari.

An dai tsare jagoran 'yan adawar da wasu mutane biyar 'yan jam'iyyar United Party for National Development na tsawon makonni biyu, a kan abinda kungiyar ta Amnesty ta ce laifi ne na tsare hanya, ba wai cin amanar kasa ba.

Kungiyar ta Amnesty, ta yi kiran da a gudanar da binciken da mutanen suka yi zargin cewa an azabtar da su.

Cin amanar ƙasa tuhuma ce da ba a bayar da beli a Zambia, kuma ana iya ɗaure mutum mafi ƙaranci shekara 15 ko kuma ma hukuncin kisa.

Da ma dai Hichilema na fuskantar tuhume-tuhume a kan tunzura jama'a su yi bore tun a watan Oktoban bara, matakin da jam'iyyarsa ta ce yunƙuri ne na rufe masa baki.

Labarai masu alaka