Obama da Jega ne suka kayar da ni a zaben 2015 - Jonathan

Jonathan da Obama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jonathan ya ce Obama ba ya son ya ci gaba da mulkin Najeriya

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ne suka sa ya sha kaye a zaben 2015.

Mista Jonathan ya bayyana haka ne a cikin wani littafi mai suna Against The Run of Play wanda fitaccen mai sharhi a jaridar This Day Olusegun Adeniyi ya wallafa.

Ya ambato tsohon shugaban na Najeriya na cewa Shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama da jami'an gwamnatinsa sun bayyana masa karara cewa suna son sauyin gwamnati a Najeriya kuma za su iya yin komai domin cimma hakan.

Ya kara da cewa hakan ne ya sa ma suka turo jirgin ruwa yaki a gabar tekun Guinea domin nuna masa da gaske suke yi.

Mista Jonathan ya ce ba anan kadai Amurka ta tsaya ba wajen yunkurin kifar da gwamnatinsa, har ta kai Shugaba Obama ya shawo kan firaministan Burtaniya David Cameron ya mara masa baya duk da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Jonathan da Cameron.

Tsohon shugaban ya ce bai fahimci irin yadda Amurka ta himmatu wajen tumbuke shi daga kan mulki ba sai da ta sa shugaban kasar Faransa Faransuwa Hollande shi ma ya bi sawunsu ana makonni kafin a yi zabe.

A cikin gida kuma, tsohon shugaban ya ce shugaban hukumar zabe na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya yi masa abin da bai yi tsammani ba, saboda har yanzu nan ya kasa fahimtar abin da ya sa Jegan ya nace cewar ya shirya wa yin zabe lokacin da kashi 40% bisa dari na masu zabe ba su karbi katinsu na zabe ba.

Ya ce ya gana da shugaban hukumar zabe ya bayyana masa damuwarsa kan yi zaben a watan Fabrairun 2015, amma ya kafe cewar ya shirya wa zaben domin Amurkawa sun ingiza shi abin da ba za taba yi a kasarsu.

Mr Jonathan ya ce hatta shugaban jam'iyyarsa ta PDP a wancan lokacin Ahmad Adamu Mu'azu ya bi sahun masu kulla masa makirci, domin saboda dalilai wadanda Mu'azun kadai ya sani, ya yi masa zagon kasa domin 'yan adawa su samu nasara kansa.

Ya kara da cewar lalle ya ji an yi masa zamba cikin aminci lokacin da ya ga irinsa sakamakon da ke fitowa daga jihohin arewa inda watakila saboda dalilai na kabilanci har jami'an tsaro suka hada baki da 'yan adawa aka fitar wani sakamakon zabe na karya kansa.

Da marubucin ya tabo masa maganar almundahana da ake zargin ta yi katutu a lokacin mulkinsa sai Mista Jonathan ya yi watsi da zargin a zaman jita-jita kawai wadda 'yan adawa, da kungiyoyin farar hula suka kururuta ta kafafen watsa labaran kasar.

Ya ce ya kafa kwamitoci hudu domin bincikar zargin da ake yi wa ministarsa ta mai Diezani Alison-Madueke, inda aka samu sabani tsakanin wasu shugabannin kwamitocin, wato Nuhu Ribado da Steve Aronsanye.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Goodluck Jonathan ne shugaba mai ci na farko da ya fadi zabe a Najeriya

Mista Jonathan ya ce ta ya ya za a yi ya yi aiki da rahoton wadanda suka kawo shi ke jayayya da juna.

Tsohon shugaban ya ce yana bakin cikin yadda ake yi wa mai dakinsa bita-da-kulli kuma shi ba zai je wata kasar waje ya ce 'yan Najeriya sun fi kowa tafka cin hanci ba domin hakan ba zai yi wata rana ba, kuma idan ya ce haka kenan har da shi.

'Yan Boko Haram sun daga wa Buhari kafa

Dangane da yaki da Boko Haram kuma ya ce ya yi iya kokarinsa da sojoji wajen murkushe ta.

A cewarsa a lokacinsa, mayakan Boko Haram na fada ne da gwamnatin kafiri, amma yanzu dole suka kwance damara domin ba za su iya kiran Buhari kafiri ba, kuma suna jin yanzu nasu ne a wajen.

Tuni dai fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa domin mayar da martani ga wasu daga cikin kalaman Mr. Jonathan a cikin wannan littafin inda ta ce Shugaba Buhari bai yi wa kowa bi-ta-da-kulli a yakin da rashawa illa dai kawai ya kan bar doka ta yi aiki kan kowa.

Shi ma ofishin jakadancin Amurka a Najeriya cewa ya yi zaben da aka yi shugaba Muhammadu Buhari zabi ne da nuna abin da 'yan Najeriya ke so.

Shi kuwa tsohon shugaban jam'iyyar PDP Ahmad Adamu Mu'azu ya shaida wa marubucin littafin cewa ya kasa yarda cewa Mr Jonathan zai yi masa irin wannan zargin wanda ya kira maras tushe balle makama.

Adamu Mu'azu ya ce amma yana ganin laifinsa shi ne wasu sun bukace shi da ya zagi Buhari lokacin yakin neman zabe ya ki don inji shi ba a yi masa tarbiyyar zagin mutane ba musamman manya.