An yi gasar ɓaunar da ta fi kyau a Pakistan

Hausawa na yi wa bauna kirari na saniyar sake Hakkin mallakar hoto WIKIMEDIA/JUGNI
Image caption Hausawa na yi wa bauna kirari na saniyar sake

Akalla ɓauna 200 aka tara domin gudanar da gasar wacce ta fi kowacce kyau a kasar Pakistan.

Jaridar Dawn newspaper ta kawo rahoton cewa manoma da makiyaya ne suka hallara a birnin Mingora, babban birnin gundumar Swat da ke arewacin Pakistan, a wani taro da aka gudanar na kwana uku domin bunkasa harkar kiwo.

Taron, wanda hukumar raya kasashe ta Amurka USAID ta shirya, kuma hukumar bayar da agaji ta farar hula ta kasar ta sanya tsabar kudi naira 75,000 ga wacce ta zo ta daya.

Laiq Badar ne ya samu nasarar samun kudin, wanda ya nuna farin cikinsa da samun nasarar da baunarsa ta yi inda ya shaida wa jaridar Dawn da cewa, "Ina da bakane goma da nake kiwonsu a wuri daya wadanda su ne hanyar da nake samun abin biyan bukatuna na yau da kullum.

Wani jami'in hukumar kula da dabbobi Muhibullah Khan, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Pakistan APP cewa, kiwon bauna na da fuskoki nau'i-nau'i, kuma babbar manufar wannan taron shi ne, "wayar da kan jama'a da kuma nunawa mutane muhimmancin kiwon wannan kyakkyawar dabba."

Wannan ne karo na farko da aka taba gabatar da gasar baunar da tafi kowacce kyau a Pakistan.

A yankin Swat kawai ake samun baunar, kuma an ce a yankin ne kawai ake samun sanyi da za a iya kiwonsu a wurin, saboda haka ne masu dabbobin ba sa sayar da su ko yankawa idan lokacin sanyi ya karato.

A cewar jaridar, wadanda suka kware a gasar ta garin Mingora sun ce ba ya ga kyau da dabbobin suke da shi, suna samar da madara da kuma wadataccen nama.

Labarai masu alaka