Barcelona da Madrid sun yi ruwan kwallaye

Messi lokacin da ya zura kwallo a raga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallo biyu da Messi ya ci suka sa ya zama kwallo 49 ya ci a bana a wasa 48

Lionel Messi ya zura kwallo biyu a raga a wasan da Barcelona ta ci gaba da jan ragamar La Liga, inda ta sa Osasuna ta fadi daga gasar da ci 7-1, yayin da Real Madrid ta ci Deportivo La Coruna 6-2.

Masu rike da kofin yanzu suna da maki 78 daidai da abokan hamayyarsu Real Madrid, wadda ita ma ta bi Deportivo La Coruna gida ta doke ta 6-2, amma kuma Madrid din tana da kwantan wasa daya.

Messi ne ya fara daga raga da kwallonsa ta 501 da ya ci wa Barca kafin Andre Gomes shi ma ya ci tasa.

Messi ya fara ci ne a minti na 12, da kuma na 61, sai André Gomes wanda shi ma ya zura biyu a ragar bakin a minti na 30 da na 57.

Alcácer shi ma ya zura biyu ne a minti na 64 da kuma minti na 86, yayin da Mascherano ya ci tasa da fanareti a minti na 67.

Roberto Torres ya karfafa wa bakin guiwa da kwallo daya a minti na 48.

Sakamakon ya sa Osasuna ta fadi kenan daga La Liga kasancewar Leganes ta doke Las Palmas har 3-0.

Wasan Deportivo La Coruna da Real Madrid

Morata ne ya fara ci wa Madrid kwallo a minti daya da shiga fili , sai Rodríguez ya biyo baya a minti na 14 da kuma minti na 66.

Vázquez ya zura tasa ana shirin tafiya hutun rabin lokaci a minti na 44, sai Isco a minti na 77, yayin da Casemiro ya cika ta karshe a minti na 87.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Madrid sun yi wasansu ne bayan Barcelona sun ci gaba da jagorancin tebur da nasararsu kan Osasuna 7-1

Amma kuma masu masaukin bakin sun samu damar zura kwallonsu ta hannun Andone a minti na 35, kafin kuma can a minti 84 Joselu ya ci musu ta biyun.

Idan dai har Real Madrid ta ci dukkanin wasanninta da suka rage to ita za ta dauki kofin La Liga na bana.

Real Madrid za ta yi wasanta na gaba a gida da Valencia ranar Asabar, kafin wasanta na farko a gida da Atletico Madrid na kofin Zakarun Turai ranar Talata.

A nata wasan na La Liga Valencia ta sha kashi da ci 3-2 a hannun bakinta Real Sociedad.