Mutuwa ta ɗau ma'auratan da suka shekara 69 tare

Illinois Couple Hakkin mallakar hoto FAMILY HANDOUT
Image caption Mutu ka raba....ma'auratan sun haɗu da juna ne tun a Argentina

Wasu ma'aurata a jihar Illinois ta Amurka da suka shafe shekara 69 a tare sun mutu sa'a ɗaya a tsakanin juna.

Jaridar Daily Herald ta ruwaito cewa Isaac Vatkin, mai shekara 91, yana riƙe da hannun matarsa Teresa mai shekara 89, a lokacin da ta ce ga-garinku-nan sakamakon cutar susucewa ta Alzheimer a ranar Asabar.

Isaac kuma ya bi ta bayan minti 40. Dangin mamatan sun ce zuciyarsu ta yi fari da suka samu labarin cewa ma'auratan sun mutu suna tare da juna.

Wani jika a wajen ma'auratan, William Vatkin ya ce "Rasuwarsu abin takaici ce, amma wanne fata za ka yi musu da ya wuce wannan?"

Hakkin mallakar hoto FAMILY PHOTO
Image caption Vatkins a ranar aurensu

'Yarsu, Clara Gesklin ta faɗa yayin jana'izar haɗin gwiwa da aka yi wa mamatan cewa "Suna matuƙar son juna, ɗaya ba zai iya rayuwa ba tare da ɗayan ba."

Limamin da ya jagoranci jana'izarsu a tsaunukan Arlington da ke wajen birnin Chicago, Barry Schechter ya ce "Suna ƙaunar juna ko da yaushe, to ga shi ma har ƙarshen rayuwarsu."

Ma'aikatan asibitin Highland Park sun fahimci jikkunan ma'auratan sun yi tsanani kuma da ƙyar suke numfashi a ranar Asabar don haka suka ba su gado a kusa da juna.

Danginsu sun ɗora hannuwansu a kan na juna kafin mutuwarsu.

'Ya'yansu sun ce ma'auratan na da ɗa uku kuma sun shaƙu da jikokinsu.

Labarai masu alaka