'Ba mu kwashi takardun kasafin kuɗi a gidan Goje ba'

Danjuma Goje Hakkin mallakar hoto NIGERIAN SENATE
Image caption Wasu na ganin al'amarin dai ka iya ƙara janyo jinkiri wajen zartar da kasafin kuɗin shekara ta 2017

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke cewa jami'anta sun kwashe wasu takardun kasafin kuɗin 2017 yayin samamen da suka kai gidan Sanata Danjuma Goje.

A wata sanarwa da suka fitar, 'yan sandan sun ce sun kai samame ne gidan Sanatan bayan sun samu bayanan sirri da ke cewa ana shirin fitar wasu maƙudan kuɗi da ake zargin na sata ne.

Ta ce kuma ba ta yi hakan ba, sai da ta samu izinin gudanar da bincike daga kotu.

Shi dai Danjuma Goje wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Nijeriya, ya ce kasafin kudin kasar na bana zai samu jinkiri don kuwa 'yan sanda sun kwashe wasu muhimman takardu a gidansa.

Ya bayyana haka ne a zauren majalisar inda ya faɗa wa takwarorinsa batun samamen da 'yan sanda suka kai gidansa da ke Abuja a makon jiya.

A cewarsa kasafin kudin da kwamitinsa ke aiki a kai na cikin kwamfutocin da 'yan sanda suka dauke a lokacin da suka kai samamen.

Batun dai ka iya kara kawo cikas ga kasafin kudin na bana, wanda tuni aka samu jinkiri wajen amincewa da shi.

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption 'Yan sandan sun ce babu gaskiya a kalaman Sanata Goje

Rundunar 'yan sanda ta zayyana abubuwan da ta gano da suka haɗar da kuɗi da takardu da kuma kwamfiyutar tafi-da-gidanka.

Ta ce a ciki babu wani abu da ya shafi takardun kasafin kuɗin shekara ta 2017, kuma duk mai sha'awa yana iya zuwa ya duba.

Sanarwar ta ce a binciken da ta gudanar ta gano kuɗi Naira miliyan 18 da oriya. Sai kuma Dalar Amurka kusan 20,000.

Haka kuma akwai Riyal na Saudiyya 9,400 da kuma wasu takardun ambulan da ke ƙunshe da fayel-fayel.

A cewarta fayel-fayel ɗin sun haɗar da bayanan ayyukan Sanata Danjuma Goje lokacin da yake gwamna da kuma na harkokin kasuwancinsa.

Sun ce sun kuma gano wasu rubuce-rubuce a wani fayel da ke nuna yadda "[tsohon] Gwamnan [Kano] Ibrahim Shekarau ya kitsa kisan da aka yi wa Sheikh Ja'afar".

Sun nanata cewa babu wasu takardu da suka danganci kasafin kuɗin shekara ta 2017 kuma tana da bidiyo da ta ɗauka yayin binciken.

Wasu na ganin wannan batu ba zai tsaya a nan ba domin majalisar dattawan ta mika shi gaban wani kwamitinta domin ya yi bincike.

Labarai masu alaka