China na amfani da fatar jaki a magunguna

Jaki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana fargabar raguwar jakuna a duniya

Wata sabuwar kasuwar bayan fage ta fatar jaki ta fara bunkasa a daidai lokacin da kasuwancin hauren Giwa da aka haramta ke ci gaba da addabar wasu yankunan kasashen Afrika.

Bukatar fatar Jaki na karuwa musamman a kasar China, inda ake amfani da ita wajen hada magungunan gargajiya.

Wani kiyasi ya nuna cewa Jakunan da ke doron kasa sun ragu cikin shekaru 20, wanda hakan ke kawo cikas a al'amura a karkara, yankunan da suka dogara da Jakuna wajen aikin gona, da sufuri da sauransu.

Wakiliyar BBC Nomsa Maseko ta ziyarci wata kasuwar bayan fage ta fatar jaki a yammacin birnin Johannesburg da ke Afrika ta Kudu.

Warin fatun jakunan da aka jeme ya lullube wurin kuma akwai akalla fatu sama da dari da aka baza.

Ana dai safarar fatun a asirtace a wata gona kusa da wani kogi kuma kasar China za a kai su.

Mutanen da suke zaune a kewayen wurin sun shaida wa wakiliyar BBC cewa kusan shekaru biyu kenan da aka fara haramtaccen kasuwancin, sannan kuma wari da hamamin yana matukar damunsu sai dai babu yadda za su yi.

Victoria Mkhize ta ce "Ba zan iya kwatanta yadda warin ya ke ba, tun da aka fara harkar nan nake sinitirin asibiti dan karbo maganin ciwon kirji, kuma sanadiyyar shakar warin na same shi. Gaskiya ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba."

Wani kitse mai danko da ake samu a cikin fatar ta jaki ta zamo tamkar zinariya a China saboda yadda ake bukatarsa dan hada magunguna.

Kobe Montsho mazaunin wani kauye ne mai suna Hebron da ke kudancin kasar Afrika ta Kudu kuma ya dogara da jakinsa wajen dibar kasa da tarkacen kayan da aka daina amfani da su dan saida wa masana'antu su sake sarrafa su.

Ta hakan ne kuma yake samun abin da zai kula da iyalinsa "Yan China ne ke biyan bata-gari don su sace jakunanmu, an sace min jakuna guda biyar, idan na rasa sauran biyar din da nake da su, ban san ta yadda zan ciyar da iyalina ba. Jakunan kadai na dogara da su."

Ana ci gaba da samun yawaitar kasuwancin fatar jaki a wasu kasashen Afrika, inda kasuwar ta bayan fage ke habaka.

Ashley Ness wata mai bincike ce a hukumar kula da dabbobi "Kasuwancin yanka jakuna ba bisa ka'ida ba ya zama wani gagarumin abu da ke kawo kudi, ba wai a Afrika ta kudu ba har da kasashen Kenya da Tanzania da Habasha da sauransu."

Ta kara da cewa "Amma a yanzu sauran kasashen Afrika sun fara nuna damuwa kan yadda Jakunansu ke raguwa. Kuma tuni kasashen Nijar da Burkina Faso suka haramta safarar jakunan ko fatarsu, muna fatan sauran kasashe zasu shiga gangamin da ake yi dan magance matsalar baki daya."

Labarai masu alaka