Man City za ta gane kurenta kan Pellegrini

Pep Guardiola (a hagu) da Manuel Peelegrini Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pep Guardiola (a hagu) ya dauki kofi uku-uku na gasar lig da Barcelona da kuma Bayern Munich

Halin da Manchester City ta samu kanta a ciki karkashin kociyanta Pep Guardiola ya nuna cewa kungiyar ba ta darraja tsohon kociyanta Manuel Pellegrini ba, in ji tsohon dan bayanta Martin Demichelis.

Tsohon dan wasan na Manchester City ya ce, idan aka duba halin da City take ciki a yanzu za a ga cewa ba wai kawai don kana da kwararren kociya sai ka samu komai cikin sauki ba.

Demichelis ya kara da cewa sannu a hankali kowa zai mutunta aikin da Manuel Pellegrini ya yi Manchester City.

A shekararsa ta farko a Manchester City bayan da ya dawo daga Malaga a watan Yuni na 2013, Pellegrini ya dauki kofin Premier da na Lig.

Ya kuma jagoranci City ta kammala a matsayin ta biyu a tebur, a bayan Chelsea a kaka ta gaba, ya kuma jagoranci kungiyar zuwa wasan kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai kafin kwantiraginsa ya kare a bazarar 2016.

Demichelis ya ce a matsayin Pellegrini na kociya dan kasar waje, a ce ya je Ingila ya dauki kofin Premier a shekarar farko, wannan ya nuna muhimmancinsa.

Bayan Manchester City Demichelis, ya kuma yi wasa karkashin jagorancin Pellegrini a kungiyar River Plate da Malaga.

Yayin da ya rage wasa shida a kammala Premier bana City ke maki 11 a bayan Chelsea ta daya a tebur, abu ne mai wuya Guardiola ya kwatanta nasarar da Pellegrini ya cimma.

Yanzu dai ta tabbata a karon farko a aikinsa na kociya Guardiola zai kare wata shekara ba tare da ya dauki wani kofi ba