Gerrad zai yi kociyan matasan Liverpool

Steven Gerrard (left) returned to Anfield as a youth coach in early 2017 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Steven Gerrard (a hagu) ya koma Anfield a matsayin kociyan matasa a farkon 2017

Tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ya ce lokaci ya yi da zai matsa gaba ya yi kocin kungiyarsa, bayan an tabbatar masa cewa zai horad da yi kociyan 'yan wasan kungiyar 'yan kasa da shekara 18.

Tsohon kyaftin din na Ingila, wanda ya yi wa Liverpool wasa sau 710 a cikin shekara 17 da ya yi zai maye gurbin Neil Critchley, kociyan 'yan kasa da shekara 18 din, wanda shi kuma zai kula da kungiyar 'yan kasa da shekara 23.

Gerrard, mai shekara 36, ya koma Liverpool ne a matsayin kociyan matsa a watan Fabrairu bayan da ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa a shekarar da ta wuce.

A lokacin da yake wasa a Anfield, Gerrard ya ci kwallo 186 kuma ya taimaka wa kungiyar ta dauki manyan kofuna takwas, da suka hada da Kofin Zakarun Turai na 2005, lokacin da kwallon da ya ci a wasan karshe ta ba wa kungiyarsa kwarin guiwa ta farfado ta doke AC Milan.

Bayan ya bar Liverpool a karshen kakar 2014-15 , ya koma LA Galaxy ta Amurka, inda ya ci kwallo biyar a wasa 34 a kaka biyu da ya yi kafin ya yi ritaya.

Haka kuma ya yi wa Ingila wasa 114, inda ya yi 38 a matsayin kyaftin, abin da ya sa ya zama na hudu a wadanda suka buga wa Ingila wasa.