Tsohon dan wasan Gabon Moise Brou Apanga ya mutu a fili

Dan wasa baya Moise Brou Apanga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Moise Brou Apanga ya yi wa Gabon wasa 33 da suka hada da na gasar cin Kofin Afirka karo biyu

Hukumar kwallon kafa ta Gabon ta bayar da sanarwar mutuwar da wasan baya na kasar Moise Brou Apanga sakamakon bugun zuciya.

A sanarwar da hukumar ta bayar ta rasuwar Apanga, mai shekara 35, ta ce ya rasu ne a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta yanzu Canon de Libreville, ranar Alhamis.

Dan wasan bayan haifaffen kasar Ivory Coast ya yi wasa a Turai a kungiyar Brest ta Faransa da kungiyoyin Perugia da Brescia na Italiya, bayan ya fara wasansa na kwararru a Romania.

Ko da yake an haifi Brou Apanga a Ivory Coast amma lokacin da ya fara zuwa kungiyar tasa ta yanzu Canon de Libreville ko FC 105, kociyansu na lokacin Alain Giresse ya shawo kansa ya koma dan kasar Gabon.

Daga nan ne kociyan da Faransa ya fara sa shi a wasan kungiyar kasar ta gabon a shekarar 2007, kuma ya taimaka masa ya tafi kungiyar Brest.

Apanga ya yi wa Gabon wasa a gasar cin Kofin Kasashen Afrika a shekarar 2010 da 2012.

Kyaftin din Gabon Pierre Emerick Aubameyang ya bayyana ta'aziyyarsa ta rashin dan wasan a shafinsa na Twitter, inda ya ce ''mun yi wasa tare, mun kuma kara a wasa a kungiyoyinmu daban-daban, amma abin farin ciki ne kasancewa tare da kai a ko da yaushe, Allah Ya jikanka dan uwana.