Fifa ta ci tarar Brazil da Argentina kan kyamar 'yan luwadi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fifa ta ci tarar kasashe da dama a kan amfani da tartsatsin wuta da wakokin kyamar masu neman jinsi daya a filin wasa

Fifa, ta ci tarar hukumomin kwallon kafa na Brazil da Argentina da Mexico a kan samun magoya bayansu da laifin wakokin kyamar masu neman jinsi daya a lokacin wasannin neman zuwa gasar Kofin Duniya na 2018.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta ci tarar Brazil fan 27,248 yayin da ta ci tarar Argentina 15,565, sannan ta ci tarar Mexico fan 7,781.

Fifa ta ce tarar ta wanna laifi ne na rera wakokin tsanar masu neman jinsi daya da kuma sauran abubuwa na rashin da'a da 'yan kallonsu suka yi.

A sanarwar da ta fitar Fifa din ta ce, sun aikata laifin ne a lokacin wasannin baya-bayan nan na neman tikitin zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2018, amma ba ta fayyace wadanna wasanni ba ne.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Albania Fifa ta ci tararta fan 77,945 bisa laifuka da dama da magoya bayan kungiyar wasan kasar suka yi a lokacin wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya da Italiya ta doke su a gidanta ranar 24 ga watan Maris.

Laifukan sun hada da jefa abubuwan tartsatsin wuta cikin fili, lamarin da ya kai ga tsayar da wasan na wasu mintina.

Ita ma Iran an ci ta tararta fan 39,015, saboda magoya bayanta sun yi amfani da abubuwan tartsatsin wutar a filin wasan da ke makare da 'yan kallo lokacin wasansu da China.

Su ma kasashen Bosnia da Herzegovina da Poland da kuma Montenegro Fifa ta ci tararsu saboda 'yan kallonsu sun irin wannan laifi na amfani da abubuwan tartsatsin wuta a filin wasa.