An tashi wasan Man City da Man United ba armashi

Marouane Fellaini ya samu jan kati Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marouane Fellaini ya samu jan katinsa na uku a Premier kuma na biyu a Manchester United

Manchester United ta ci gaba da zama a matsayinta na biyar a teburin Premier bayan wasanta da abokiyar hamayyarta Manchester City, wanda suka tashi ba ci a Etihad, amma an kori Fellaini.

United tana da maki 64 a wasa 33 yayin da Manchester City ta hudu a tebur take da maki 65, ita ma a wasa 33.

Saura minti shida a tashi daga wasan alkalin wasa ya kori Marouane Fellaini, wanda bai dade da samun katin gargadi ba saboda keta da ya yi wa Aguero, bayan da ya sake yi wa Sergio Aguero karo.

United wadda take maki biyu a bayan Liverpool ta uku da kwantan wasa daya, ta yi wasa 24 kenan na Premier ba tare da an doke ta ba.

Wasanta biyu daga cikin biyar da suka rage za ta yi su ne a waje, a gidan Arsenal ranar 7 ga watan Mayu da kuma gidan Tottenham ranar 14 ga watan Mayu.

Manchester City wadda za ta gama kakar farko da Pep Guardiola ba tare da kofi ba tana maki daya tsakaninta da Liverpool, amma tana da kwantan wasa daya