Al'ummar Kano na fama da ƙamfar ruwan sha

Wasu jama'a kenan yadda suke wahala wajen samun ruwa Hakkin mallakar hoto TOMMY TRENCHARD / IFRC
Image caption Al'ummar birnin Kano na kokawa da matsalar karamcin ruwan sha da ta addabesu shekara da shekaru

Al'ummar birnin Kano sun auka cikin matsalar ƙarancin ruwan sha, inda unguwanni da dama suka koma amfani da ruwan rijiya da na famfon tuƙa-tuƙa.

A lokuta da dama waɗannan kafofi ba su da ingantaccin tsafta don haka akwai kasadar yaɗuwar cutukan da ake bazuwa ta hanyar ruwa.

Wani magidanci Malam Hamisu a unguwar Agadasawa ya ce suna matsalar ruwan sha sosai duk da yake akwai kawunan famfo.

Ya ce "sai mu shekara ruwa(n famfo) bai zo mana unguwar nan ba. Ya ce muna sayen ruwa ne daga masu kurar ruwa kuma suna sayar da jarka ɗaya kimanin Naira 30."

A cewarsa, ɗawainiyar ta yi yawa. "Ina da mata ɗaya da yaro shida."

Shi ma wani Rabi'u ya ce matsalar ƙarancin ruwan ta yi tsanani don kuwa sukan niƙi-gari zuwa wasu unguwanni don taro 'yan ga-ruwa.

Kasuwar 'yan ga-ruwa ta buɗe

Wani mai gidan sayar da ruwa mai suna Buhari a yankin Ƙofar Nassarawa ya ce suna matuƙar ciniki, ya ce a rana yakan sayar da ruwa na kimanin naira dubu uku zuwa sama.

Shi ma wani ɗan ga-ruwa, Malam Abdu Ƙyaure ya ce yana kai ruwa unguwannin da suka haɗar da Sabuwar Ƙofa da Sharaɗa da ƙofar Nassarawa da kuma Sokoto road.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, Alhaji Sule Riruwai ya ce na'urorin tura ruwa da ake da su zuwa birnin Kano na buƙatar gyara.

Ya ce a cikin na'ura takwas da ake ita a Kano, guda uku ne kacal ke aiki wurjanjan. Ko da yake, nan da mako uku za su kammala gyare-gyare.

Kwamishinan ya kuma zargi masu aikin kwasar yashi a koguna da karkatar da akalar ruwa saboda aikace-aikacensu.

Labarai masu alaka