"Ya kamata 'yan sanda su fayyace wanda ya kashe Sheikh Ja'afar"

Danjuma Goje Hakkin mallakar hoto NIGERIAN SENATE
Image caption Batun dai ya taso ne bayan shekara goma da kashe Sheikh Ja'afar Adam a Kano

Sanata Danjuma Goje ya buƙaci rundunar 'yan sandan ƙasar, ta fito ta bayyana gaskiya kan mutanen da suka kashe malamin addinin musulunci Sheikh Ja'afar Muhd Adam.

Shugaban kwamitin kasafin kuɗi a majalisar dattijan Nijeriya, sanata Danjuma Goje ya ce ya yi wannan kira ne saboda yadda ake ƙoƙarin goga masa kashin kaji.

Ya ce "Amma na haƙiƙance ba ni da wani alaƙa da takardar da ta shafi wai yadda Shekarau ya tsara halaka marigayi Sheikh Ja'afar..."

A cewarsa "'Yakamata ace 'yan sanda su suka fi kowa sanin wa ya kashe Sheikh Ja'afar, kuma ko wa ya tsara."

Sanata Goje na mayar da martani ne a kan bayanin da rundunar 'yan sandan ta yi game da kuɗi da takardun da ta gano yayin samamen da ta kai gidansa.

'Yan sanda sun ce a cikin takardun akwai wani fayel mai ɗauke da rubutu a kan kashe Sheikh Ja'afar Adam a Kano, har ma sun ambaci sunan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tuni dai wannan bayani ya janyo gagarumin ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta a tsakanin 'yan Nijeriya.

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci yayin sallar asubah a Kano.

Danjuma Goje dai ya ce bayanin 'yan sanda wani yunƙuri ne kawai na shafa masa kashin kaji "don a cuce ni."

Ya ce yana wannan magana ce don ya lura da yadda ake son ɓata masa suna. "A manna mini abin da ba gaskiya ne."

Ya zuwa yanzu dai tsohon gwamnan jihar Kanon Malam Ibrahim Shekarau bai ce komai game da batun ba.

Labarai masu alaka