Ko wayar salula na iya warkar da ciwon suga?

Smartphones to treat Diabetes Hakkin mallakar hoto JSHAO
Image caption Ta hanyar shafa fuskar wayar salular ana iya gane yawan sukarin da ke cikin jini

Masana kimiyya sun yi amfani da wayar salula ta smartphone don sarrafa aikin ƙwayoyin halitta a jikin wata dabba.

An haɗa kimiyyar rayuwar halittu ce da fasaha don sarrafa yawan sukari a cikin jinin wani ɓera mai fama da ciwon suga.

Ana iya amfani da wannan dabara wadda aka bayyana a mujallar kimiyya ta Translational Medicine wajen duba lafiyar masu fama da cutuka iri daban-daban.

Masu binciken na ƙasar China sun ce dabarar ka iya buɗe wani sabon babi a fannin ba da magani.

Gwajin dai ka iya taimaka wa miliyoyin mutane masu fama da ciwon suga a faɗin duniya ta hanyar taƙaita yawan sugan da ke cikin jini.

Sinawa masu bincike sun ce sun ƙera wasu ƙwayoyin halittu da ke daidaita sinadarin sukari a cikin jinin ɓera ta hanyar amfani da wata 'yar fitila mai haske.

Manhajar wayar salula ce ke sarrafa fitilar daga nesa bayan ta karɓo bayanai daga wata 'yar na'urar ƙididdige adadin suga a cikin jini wadda aka maƙala wa ɓeran.

Mataki na farko ana sauya ƙwayoyin halittun jiki zuwa wasu masana'antu.

An sarrafa sigar ƙwayoyin gadon halittun don samar da magungunan da za su iya taƙaita ƙaruwar suga a cikin jini.

Ana kiran wannan fasaha a kimiyyance da optogenetics kuma ƙwayoyin halittu kan faɗa aiki wurjanjan da zarar an dallare su da wani jan haske.

Fasahar dai tana amfani da wani ɗan ƙanƙanin ƙwan lantarki da kuma wata manhajar wayar salula da ke sarrafa shi.

Masu binciken a jami'ar East China Normal da ke Shanghai kan dasa wannan fasaha ce a jikin ɓera, ta yadda za su iya daƙile ciwon suga ta hanyar ɗan taɓa fuskar wayar.

Hakkin mallakar hoto JSHAO
Image caption Ana iya maƙala 'yar na'ura a ƙarƙashin fata don sadarwa a tsakani

Ayarin masu binciken ya ce nazarin "ka iya share fagen wani sabon babi na ba da magani gwargwadon buƙatar mutum ta hanyar fasahar dijital da za ta karaɗe duniya.".

Masana kimiyyar na buƙatar ɗiban wani ɗan ɗigon jini don sanin yawan sugan da ke cikinsa ta yadda za su iya ƙididdige adadin maganin da jiki yake buƙata.

Babban burinsu shi ne ɓullo da wani cikakken tsarin amfani da na'ura don gano yawan sugan da ke cikin jini da kuma daidai kimar sinadarin laƙani da za a bayar.

A bayyane take cewa fasahar tana wani matakin farko ne, amma dai ba za ta taƙaita ga magance ciwon suga ba. Ana iya sarrafa ƙwayoyin halittu ta yadda za su iya haɗa magunguna iri daban-daban.

Wani masanin kimiyyar rayuwar halittar curin sinadari, Farfesa Mark Gomelsky a Jami'ar Wyoming, ya ce nazarin wani "cikar buri ne mai sa shauƙi".

Ya ƙara da cewa: "Nan da yaushe ne za mu sa ran ganin mutane na tafiya a kan titi sun ɗaura 'yar wata fitila a hannunsu da za ta riƙa dallare ƙwayoyin halittun jiki da za su samar da wani magani da ƙwayoyin halittun gado suka sarrafa, ta hanyar amfani da wayar salula?

Labarai masu alaka