Zan iya zuwa kotu a kan ɓata-suna - Shekarau

Ibrahim Shekarau
Image caption A zamanin mulkin Ibrahim Shekarau ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin Sheikh Ja'afar Adam a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano a Nijeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yana bin kadin ɓata-suna da 'yan sandan ƙasar suka yi masa.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta gano wata takarda da ke alaƙanta Shekarau da kashe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam.

A cewarta jami'anta ne suka gano takardar bayan wani samame da suka kai gidan sanata Danjuma Goje a Abuja.

Mai magana da yawun Shekarau, Malam Sule Ya'u Sule ya ce ba shakka suna bin bahasin wannan batu a wajen 'yan sanda.

Ya ce sun tuntuɓi 'yan sanda a kan su fito su binciko gaskiyar wannan al'amari kuma su yi wa jama'a bayani.

Sule Ya'u Sule ya ce suna iya zuwa kotu a kan wannan ɓata-suna da ya ce an yi wa Ibrahim Shekarau.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN SENATE
Image caption Sanata Danjuma Goje ya nisanta kansa da takardar kuma ya nemi 'yan sanda su fayyace gaskiya

A cewarsa, takardar da 'yan sanda suka yi iƙirarin sun gano a gidan Sanata Danjuma Goje tsohuwar takarda ce da wasu abokan hamayya suka rubuta don shafa wa Shekarau kashin kaji.

Ya ce "Ni ma ina da wannan takarda. Al'umma da yawa a Kano sun samu wannan takarda...Na tabbata wannan takarda ce wannan tsohon gwamna (sanata Danjuma Goje) ya samu. Idan kuma wata ce daban, ya kamata 'yan sanda su fito su yi wa mutane bayani."

Shi da kansa Malam Ibrahim Shekarau ne a wancan lokaci ya nemi 'yan sanda su yi bincike a kan wannan takarda.

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 ne wasu mutane suka harbe fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ja'afar Mahmud Adam yayin sallar asubah a Kano.

'A yi wa jama'a bayani'

Mai magana da yawun Shekarau ya ce 'yan sandan sun yi bincike a kai kuma sun san abin da suka gano game da batun, don haka ya kamata su fito su yi wa al'umma bayani.

Da aka tambaye shi ko Shekarau zai ɗauki matakin shari'ah a kan wannan al'amari, ya ce suna jiran bayanin 'yan sanda kafin su san mataki na gaba da za su ɗauka.

Sule Ya'u ya ce sun ji Sanata Danjuma Goje yana bayani ta kafofin yaɗa labarai inda ya tsame kansa, don haka Shekarau ya miƙa komai ga 'yan sanda.

A cewarsa waɗanda suka fito suka yi wannan batu, a wajensu suke neman bahasi amma ba Sanata Goje ba.

Ya yi shaguɓe kan yadda wasu mutane da bai bayyana ko su wane ne ba, da ya ce burinsu a kullum su ƙulla wa tsohon gwaman sharri, "su je su ci gaba da yi."

Labarai masu alaka