'Halin da Nigeria ta shiga ya ƙara mana matsin rayuwa'

Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nijar na bukatar agajin tunkarar matsalar karancin abinci

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun gudanar da wani taro da cibiyoyin ba da agaji don shawo kan matsalar ƙarancin abinci da mutane kimanin miliyan ɗaya da rabi ke fuskanta a kasar.

Ba kawai mutane ne, suka samu kansu cikin halin yunwa ba, dabbobin ƙasar ma suna cikin tasku sakamakon rashin ciyawa a Nijar.

Gwamnati ta ce faɗuwar darajar Naira da ta shafi kasuwar dabbobin ƙasar a Nijeriya da kuma rashin kasuwa a ƙasashen Libya da Aljeriya duk yi tasiri wajen sanya Nijar a wannan hali.

Ta ce tana buƙatar saifa biliyan sittin da biyu don cike giɓin abincin da mutane da dabbobi ke buƙata a faɗin ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida Malam Bazoum Mouhammed ya ce Nijar ba ta taɓa fuskantar ƙarancin ciyawa musammam a wurare kamar jihar Tawa irin na bana.

"Babbar matsalar ita ce busashenmu mu...naira ta faɗi. Nairar da a da ake canzar da jaka guda (ta saifa) naira 300, (yanzu) ta kai jaka ɗaya, naira 800.

Ya bayyana damuwa game da karayar arziƙin da makiyaya da manoman ƙasar suka samu saboda dabbobi ba sa daraja.

"Abin da muka shaida a watannin da suka gabata, shi ne ake kawo busashe daga Nijeriya a sai da su a Nijar."

Gwamnatin Nijar dai ta ce a bana ne wannan matsala ta fi ƙamari, don kuwa a baya ko an samu ƙarancin abinci, mutane ba sa shiga mawuyacin hali saboda dabbobi suna kuɗi.

Haka zalika, ana fuskantar hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar, lamarin da ya ƙara tsananta halin takura ga jama'a.

Bazoum ya ce: "Da hasashen da muka yi, har mu kai azumi kuɗin hatsi buhu guda, bai zarce jaka 20 ba, sai ga shi nan yau ya kai jaka 30."

Ya ce ƙasar tana buƙatar tan dubu arba'in da uku na hatsi don cikawa a kan abin da take buƙata tan dubu saba'in da biyar, da za a sayar cikin farashi mai rangwame.

Haka zalika, jamhuriyar Nijar na buƙatar gudunmawar abincin dabbobi har tan dubu sittin da takwas baya ga iri tan dubu goma sha biyu don raba wa manoma a cewar Bazoum.

Mahukuntan dai na danganta wannan matsala da sauyin yanayi inda a wasu yankunan ƙasar aka fuskanci fari, yayin da a wasu kuma aka gamu da ambaliyar ruwa da ta lalata albarkatun gona da kashe dubban dabbobi.

Labarai masu alaka