'Yan sanda sun kama Sule Lamido

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alhaji Sule Lamido ya na daya daga cikin jigajigan 'ya'yan jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.

Rundunar ta tabbatar wa BBC cewa an kama tsohon gwamnan ne bisa zargin ingiza magoya bayansa su dauki doka a hannunsu.

Rundunar ta ce tsohon gwamman ya yi kalaman ingiza magoya bayan na shi ne, yayin wani gangami na siyasa a jihar Jigawa.

Ta ce gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru ce ta kai koke game kalaman tsohon gwamnan, a don haka ne kuma rundunar ta dauki mataki.

An kama Sule Lamido ne a gidan shi dake Sharada a Kano da safiyar Lahadin nan.

Kawo yanzu dai tsohon gwamnan ko wani na kusa da shi bai ce komai ba game da kama shin da aka yi.

Alhaji Sule Lamido, yana daya daga cikin jigajigan 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, kuma a 'yan kwanakin nan, ya yi ta sukar irin kamun ludayin gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC.