'Ba mu yarda da auren 'yan luwaɗi a coci ba'

Catholics Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Limaman katolika a sassa daban-daban na duniya na yawan fuskantar zargin lalata da kananan yara

Wata tawaga ta bishop bishop na darikar Anglican daga nahiyar Afirka, ta ce za ta aike da wakilai zuwa Burtaniya domin neman a taka wa daura auren jinsi guda a coci burki.

Wata kungiyar gamayyar bishop-bishop masu ra'ayin mazan jiya ce mai suna Gafcom ta sanar da hakan bayan kammala wani taron da ta yi a Najeriya.

Kungiyar ta ce ba ta gamsu da yadda aka sakar wa masu neman junansu mara ba da sunan 'yanci a coci-coci.

Gafcom ta kuma ce abin da ya sa take son daukar matakin aikewa da wakilai zuwa Burtaniya, shi ne yunkurin kada kuri'a da ake son yi a Scotland dangane da daura auren 'yan luwadi da madigo a coci-cocin.

Da man dai kungiyar ta Gafcom ta ce tuni ta yanke alaka da cocin ta Anglican da ke kasashen Arewacin Amurka sakamakon wannan ta'ada.

Batun halasci ko rashinsa dangane da auren jinsi guda wani al'amari ne da aka dade ana musayar yawu tsakanin mabiya addinin kirista a duniya.

Yayin da wasu cocin da limaman ke ganin 'yancin dan adam ne da bai kamata a sarayar da shi ba, wasu na kallon al'amarin da yin karo da koriyar Yesu Almasihu.

An dai sha samun fasto fasto da ke ikrarin su masu neman maza ne, al'amarin da ya janyo musu kakkausar suka daga mabiya.