Nigeria: 'Jihohi 11 ba sa biyan albashi'

Ma'aikata a duk fadin duniya na gudanar da bikin ranar ma'aikata
Image caption Ma'aikata a duk fadin duniya na gudanar da bikin ranar ma'aikata

A ranar Litinin ce ma'aikata da 'yan kwadago a duk fadin duniya ke bikin ranar ma'aikata ta duniya.

An zabi ranar daya ga kowanne watan Mayu domin bikin zagayowar wannan rana saboda tunawa da kisan wasu ma'aikata hudu da 'yan sanda suka yi a birnin Chigaco na Amurka a shekarar 1886, yayin wani yajin aiki.

A irin wannan rana ce ma'aikata ke la'akari da irin gudunmuwar da suke bayar wa wajen ci gaban tattalin arzikin kasashensu.

Kamar sauran kasashen duniya, Najeriya ma na daga cikin kasashen da ke gudanar da wannan biki na ranar ma'aikata.

Comrade Ayuba Wabba, shi ne shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC, ya shaidawa BBC cewa, suna tuna wannan rana ce da taken, gudunmuwar da ma'aikata ke bayarwa wajen ci gaban kasa, musamman a irin yanayin da kasar ke ciki a yanzu.

Comrade Wabba, ya ce ma'aikata su ne suka fi kowa shan wahala a irin yanayin da Najeriya ke ciki a yanzu.

Saboda a cewarsa, akwai jihohi kusan goma sha daya da basa biyan albashi da biyan 'yan fansho hakkokinsu.

Shugaban kungiyar ta kwadago, ya ce za a gudanar da irin wannan biki a dukkanin jihohin Najeriya ban da jihar Kogi kadai.

Comrade Wabba, ya ci gaba da cewa, a wannan rana sun gayyato shugaban kasa da kuma 'yan majalisu, in da za a gudanar da jawabai.

Sannan kuma ya ce abin da ma'aikata ke so a yanzu shi ne, kasancewar cin hanci da rashawa ya yi wa kasar katutu, to yanzu duk wanda zai bayar da bayani a kan kamo wani wanda ya saci kudin gwamnati, to ya kamata a samar da dokar da zata bashi kariya.

Kuma idan har an samu mutum da laifin satar kudin gwamnatin, to ya kamata a cikin lokaci kankani a hukunta shi.

Daga bisani, ya yi tsokaci a kan jihohin da ba sa biyan albashi, inda ya ce duk jihohin da ba sa biyan albashi to ba mamaki ko sun ciwo bashin da ya fi karfinsu, ko kuma sun yi kwangiloli na bogi domin a yi almubazzaranci da kudaden jama'a.

Labarai masu alaka