China na abin da ya dace a kan Korea ta Arewa —Trump

Trump ya ce abinda Koriya ta Arewa ta ke yi sam bai dace ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Trump ya ce abinda Koriya ta Arewa ta ke yi sam bai dace ba

Shugaba Trump na Amurka ya yaba wa takwaransa na China, Xi Jinping, bisa kokarin da ya ke shirin yi na neman goyon bayan kasashen duniya a kan su goyi bayan yunkurin Amurka na dakatar da shirin Koriya ta Arewa na makamakin Nukiliya.

Mr Trump ya ce samun goyon bayan China wajen maganin Koriya ta Arewa yafi muhimmancin akan takura mata akan harkokin kasuwanci.

Shugaban na Amurka ya yi gargadin cewa daukar duk wani matakin soji akan Koriya ta Arewa zai janyo rasa rayukan miliyoyin mutane.

A jiya Lahadi ne Mr Trump, ya tattauna da firayim ministan Thailand da na Singapore akan hanyoyin matsawa Koriya ta arewa lamba.

A wata hira da kafar watsa labarai ta CBS, shugaban na Amurka, ya ce har yanzu akwai kuruciya a tattare da Kim Jong-un, duk da cewa sai da ya yi maganin wasu mutane da ake gani ba kanwar lasa ba ne a lokacin mulkinsa.

Wadannan kalamai na Mr Trump, na zuwa ne bayan shirin Koriya ta Arewa na gawajin makami mai linzami ya yi tutsu a karo na biyu a ranar Aasabar.

Labarai masu alaka