Ba da Yahudawa mu ke rikici ba — Hamas

Hamas ta ce ta aimince da kasar Palasdinu ta wucin gadi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hamas ta ce ta aimince da kasar Palasdinu ta wucin gadi

Kungiyar Hamas ta Palasdinawa masu gwagwarmaya da makamai, ta wallafa kundinta na farko kan sabuwar manufarta tun bayan wallafa kundin kafa ta, a wani yunkuri na jawo wa kanta kima a idanun duniya.

A cikin kundin, Hamas ta bayyana aniyarta ta amincewa da kasar Palasdinu ta wucin gadi a cikin yankunan da aka shata iyakokinsu gabanin shekarar 1967, amma ba tare da amincewa da 'yancin Isra'ila na wanzuwa ba.

Kungiyar ta jaddada cewa ba da Yahudawa take rikici ba, da wadanda ta kira masu mamayar kafa kasar Isra'ila take riciki.

Kungiyar ta ce, ta yanke alakarta da kungiyar 'yan-uwa Musulmi, a wani mataki da ake ganin na kokarin kyautata hulda da kasashen Larabawa na yankin Tekun Fasha ne.

Labarai masu alaka