Za a dinke baraka tsakanin Jamus da Rasha

Jamus dai na son ganin Rasha ta samar da zaman lafi a Syria, tun da dai ita kadai ce ke iya tsawatar wa shugaban na Syria. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamus dai na son ganin Rasha ta samar da zaman lafi a Syria, tun da dai ita kadai ce ke iya tsawatar wa shugaban na Syria

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel za ta ziyarci Rasha domin tattaunawa da shugaba Vladimir Putin kan rikicin Syria.

Ana tsammanin baya ga batun Syria, Merkel za ta kuma nemi warware batun mamaye yankin Crimea da Rashar ta yi.

Wakilin BBC a Berlin, ya ce dukkannin kasashen biyu wato Jamus da Rasha, za su amfana da wannan tattaunawa.

Misis Merkel, na bukatar Mr Putin ya kawo karshen rikicin da ake yi a Ukraine ta hanyar shawo kan 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha.

Mr Putin ya san cewa Jamus ce kadai zata iya wuce masa gaba wajen dage wa kasarsa takunkumin da aka kaka ba mata.

Ziyarar ta Angela Merkel zuwa Rasha ta zamo irinta ta farko a baya-bayan nan da wata kasar Turai ta tunkari Vladimir Putin a cikin gidansa kan rikicin Syria da ma na yankin Crimea.

To sai dai ana ganin tattaunawar tasu za ta zama makamanciyar taron masu shan shayi ne a watse domin masana na tsammanin duk abin da shugabar za ta fada wa takwaran nata zai zama kawai ta zo mu ji ta.

Alaka dai tsakanin Jamus da Rasha ta yi sakwa-sakwa tun 2014 lokacin da Jamus ta yi uwa tai makarbiya wajen kakabawa Rashar takunkumi irin na tarayyar Turai sakamakon mamaye yankin Crimea na Ukraine da Rashar ta yi.

Tun lokacin kanwar kasashen biyu ba ta jiko wuri daya kuma ko da an hadu a taruka daga hannu ne ke shiga tsakanin shugabannin biyu.

Jamus dai na son ganin Rasha ta samar da zaman lafiya a Syria, tun da dai ita kadai ce ke iya tsawatar wa shugaban na Syria.

Labarai masu alaka