Zan ci gaba da sukar Donald Trump— Hillary Clinton

Hillary Clinton ta ce yanzu za ta koma sukar wasu tsare-tsaren Donald Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hillary Clinton ta ce yanzu za ta koma sukar wasu tsare-tsaren Donald Trump

'Yar takarar shugabancin Amurkar ta jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton, ta ce da an yi zabe a ranar 27 ga watan Oktoban 2016, to da babu shakka ita ce za ta lashe zaben.

Misis Clinton ta kara da cewa ta yi iya yakin zaben da ya kamata duk wani mai neman a zabe shi zai yi, amma kuma al'amuran sai suka sauya a kwanaki goman karshe.

Hillary Clinton,ta zargi kutsen da Rasha ta yi da kuma rahoton da hukumar FBI ta fitar cewa ta yi amfani da adireshinta na imail wajen karbar sakonni lokacin ta na sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Shugaban hukumar binciken laifukan cikin gidan Amurka, FBI, James Comey ne dai ya yi wa majalisar wakilan kasar wasika cewa hukumar za ta sake bincikar zargin amfani da imail din da ba na gwamnati ba wajen karbar sakonnin gwamnati.

Yanzu haka dai misis Clinton ta ce tunda waccan dama ba ta samu ba, ta hakura ta koma cikakkiyar mai fafutukar kare hakkin 'yan kasa.

Kuma ce ta na nan a kan bakarta ta sukar tsare-tsaren abokin fafatawarta, shugaba Donald Trump, musammman wadanda suka jibanci kasashen waje da kuma yadda mista Trump din yake matukar son amfani da shafin Twitter wajen aikewa da sakonni.

Labarai masu alaka