Ko wanne hali mata maza ke ciki a Kenya?

Irin mutanen da ake haifa da halittar mata maza na fama da tsangwama a Kenya
Image caption Irin mutanen da ake haifa da halittar mata maza na fama da tsangwama a Kenya

Miliyoyin yaran da aka haifa da halittar maza ko mata, sun shafe shekaru masu yawa su na fadi-tashin zama cikin al'umma.

Irin wadannan yaran dai na fuskantar tsangwama da nuna wariya a cikin mutane, a wasu lokutan ma har hallaka su ake yi.

A cikin wasu al'umma kamar na kasar Kenya, ana kallon irin wadannan yara a matsayin wadanda za su haifar da wani bala'i a cikin al'umma, dan haka ne ma da zarar an haife su nan take ake hallakasu.

BBC, ta gano wani mutum mai suna Darlan Rukhida wanda ke da irin wannan halitta da ya buya tun ya na yaro, a yanzu kuma ya ke son fara fafutukar karbarwar 'yan uwansu masu halittu biyu 'yanci.

BBC ta tattauna da Darlan mai shekaru 42, in da kuma ya yi bayani akan tarihin yadda rayuwarsa ta kasance tun yana karami.

Darlan ya ce, an haife shi ne da halittar mata da maza, dan haka za a iya kiransa mace ko namiji, kuma yana alfahari da hakan.

Mutumin ya ce,mahaifiyarsa dai ta fi mayar da hankali kan halittarsa ta maza, dan haka ko da ya ke yaro kayan maza ta ke sanya masa, ta na kuma kaffa-kaffa da shi.

A kokarin sama wa Darlan rayuwa mai inganci, mahaifiyarsa ta samo masa maganin da zai rage tasirin halittar mata, ta kuma yi masa aure, a wannan lokacin sai rayuwa ta yi ma sa kunci.

Darlan ya ce, a wancan lokaci babu wanda ya ke son mu'amala da shi, inda a wasu lokutan ma ya kan yanki daji ya yi ta tafiya shi kadai ko ya ji sanyi a ransa.

Ya ce, a wani lokacin mutane kan yi kokarin cire masa kaya wai dan kawai su ga halittar da ke jikinsa, abin da ke matukar kona masa rai , saboda kamar wanda ya aikata wani mugun abu haka mutane ke zuwa kallon sa.

Darlan ya ce ya taba yunkurin hallaka kansa hakan bai yiwu ba.

Yanzu Darlan, ya girma, har ma ya gina wani gida domin ajiye tsofaffi da yara marayu ana kula da su a kasar Kenya.

Kuma ya ce zai ci gaba da fafutukar ganin ya kwato wa masu halitta irin ta sa 'yancinsu, domin a daina tsangwamarsu.

Labarai masu alaka