'Yan Venezuela na bukatar shugaba Maduro ya yi murabus

Masu bore a Venezuela
Image caption Tun bayan hawan shugaba Maduro karagar mulki, tattalin arzikin kasar Venezuela ya fada halin ni 'ya su

An harbe wani matashi a birnin Valencia na kasar Venezuela a lokacin da suka fito zanga-zangar adawa da gwamnatin Nicolas Maduro, wannan shi ne kisa na baya-bayan nan da aka yi wa masu boren tun bayan fara zanga-zangar makwannin da suka wuce.

Matasa a wasu biranen kasar sun fasa shagunan mutane tare da yi musu sata, ya yin da rahotanni daga jihar Zulia ke cewa an kakkabo mutum-mutumin tsohon shugaban kasar marigayi Hugo Chabez.

Akalla mutane talatin ne suka rayukansu, wasu daruruwa kuma suka jikkata tun bayan fara bore da matsawa shugaba Maduro lambar yin murabus, saboda rashin kwararan manufofi da tsare-tsaren yadda za a fitar da kasar daga matsin tattalin arziki.

Kayan bukatun yau da kullum, musamman kayan abinci sun yi matukar tsada ya yin da talauci ke neman samun wuri a kasar.

A bangare guda kuma a gobe lahadi ne wasu mata a birane da garuruwan kasar suka shirya fitowa dan yin maci, duk dai na kin amincewa da shugabancin mista Maduro.

Labarai masu alaka