An daina ganin Kanye West a shafukan sa na intanet

Kanye West
Image caption Fitaccen mawakin ya yi suna ne saboda salon wakar rap da matasa ke so kauna

Fitaccen mawakin nan dan Amurka mai salon rap Kanye West ya toshe shafukansa na sada zumunta na internet da suka hada da Twitter da Instagram.

Mawakin dai ya na da miliyoyin masoya da ke bibiyar dukkan shafukansa na sada zumunta da muhawara.

Babu dai takamaimai dalilin da ya sanya mawakin yin hakan, amma lokaci na karshe da aka ga gilmawarsa shafukan shi ne watan Nuwambar bara.

A lokacin da ya zargi takwaransa a fagen waka Jay-Z ta yunkurin hallaka shi a lokacin da ya hau kan mumbari bayan kammalawa wata waka da ya yi tare da shaidawa dumbin 'yan kallo cewa zai zabi shugaba Donald Trump a zai zaba a matsayin shugaban Amurka.

Ma'abota shafukan sada zumunta sun koka kan yadda idan suka yi kokarin neman shafin mawakin sai ya nuna musu shafin ya daina aiki.

To amma matar sa fitacciyar 'yar wasan kwaikwayo da ake watsawa a gidan talabijin din Amurka da tauraron dan adam a ranakun mako Kim Kardashian ta ci gaba da sabgogin ta kamar yadda ta saba a shafukan intanet inda ta ke da magoya baya miliyan 51.

Baya ga wasan kwaikwayo, Kim ta yi fice wajen tallata kayan adon mata da maza har da yara inda 'yar ta da mijinta ke sanyawa dan kara janyo hankali masu ciniki.

Masoyan wakokin sun roki Kim ta roki mijinta ya dawo shafukan sa, dan sun yi kewarsa matuka.

Labarai masu alaka