Manchester City ta wulaƙanta Crystal Palace

Kompany ya koma kan ganiyarsa tun da ya gama jinya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kompany ya koma kan ganiyarsa tun da ya gama jinya

Manchester City ta jaddada matsayinta na zama cikin hudun farko a saman tebirin Premier bayan ta doke Crystal Palace da ci 5-0.

Hakan ya sa ta zama ta uku, kuma ta sha gaban Liverpool da bambancin yawan maki.

David Silva ne ya zura kwallon farko minti biyu da soma wasa.

City ba ta sake zura kwallo ba kafin a tafi hutun rabin lokaci duk kuwa da cewa 'yan wasan Palace ba su da tagomashi.

Palace ta kusa farke kwallon da aka ci ta lokacin da Christian Benteke ya doka kwallo da ka, sai dai mai tsaron gida Willy Caballero ya yi caraf ya cafke ta.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, 'yan wasan City suka kara kaimi, inda kyaftin Vincent Kompany ya zura tasa kwallon.

Daga bisani De Bruyne da Raheem Sterling suka zura kwallo ta uku da ta hudu, inda shi kuma Nicolas Otamendi ya cikashe ta biyar da kansa.

Labarai masu alaka