'Yan matan Chibok 82 sun isa Abuja

Shugaba Buhari ya sha alwashin ceto dukkan 'yan matan Chibok Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin ceto dukkan 'yan matan Chibok

Fadar shugaban Najeriya ta ce 'yan matan Chibok 82 da kungiyar Boko Haram ta saka ranar Asabar sun isa Abuja, babban birnin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya ce shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari ne ya karbe su a filin jirgin saman Abuja.

Wani kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok ne bayan ta mika musu wasu 'yan ƙungiyar da ke tsare a hannun jami'an tsaron kasar.

Ya kara da cewa za a mika 'yan matan ga Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa, "An yi wata da watanni ana tattaunawa da 'yan ƙungiyar tare da gudunmawar ƙungiyoyi daban-daban... da kuma ita kanta ƙasar Switzerland. Wannan tattaunawa da aka yi, sai aka cim ma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Nijeriya da su 'yan ƙungiyar, wanda gwamnati ta karɓi 'yan mata. Su kuma aka ba su wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyarsu da ke hannun gwamnatin Nijeriya a yanzu."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku saurari hira da Malam Garba Shehu

Sai dai bai fadi adadin 'yan Boko Haram din da gwamnati ta saka ba.

Ya ce ana sa ran samun cikakken jawabi game da ko 'yan Boko Haram nawa gwamnati ta bayar a madadin 'yan matan Chibok 81 daga bakin shugaban ƙasar kansa.

Da aka tambaye shi, anya gwamnati ba ta yi raguwar dabara, sakin 'yan Boko Haram da ka iya ci gaba da kai hare-haren da za su yi sanadin mutuwar rayukan 'yan Nijeriya?

Garba Shehu ya ce "Ai mu ba ma fatan haka, cewa wannan abu zai je ya kawo wata ɓarna a nan gaba."

A cewarsa irin wannan tattaunawa idan aka fara ai ba a san yadda za ta kaya ba.

Tana iya yiwuwa wannan ya zama mataki na gina ƙarin wasu yarjejeniyoyi nan gaba wataƙila sulhun da ake nema ya zama na dindindin, in ji Garba Shehu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saura 'yan matan Chibok 113 a hannun 'yan Boko Haram

A watan Afirulun shekarar 2014 ne aka sace 'yan matan 276 daga makarantarsu da ke garin Chibok na jihar Borno.

Sai dai tun a lokacin ne wasu daga cikinsu suka tsere.

Shugaban kasar wancan lokacin Goodluck Jonathan ya sha suka daga fadin duniya saboda gazawarsa wurin ceto 'yan matan.

Kafin wannan lokaci dai, sojojin Najeriya sun ceto wasu daga cikinsu, yayin da 'yan Boko Haram suka saki 21 a watan Okotoban shekarar 2016, bayan kungiyar Red Cross da gwamnatin Switzerland sun jagoranci sulhu tsakanin gwamnatin da 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Sace 'yan matan na Chibok ya janyo zanga-zanga da Allawadai a duk fadin duniya.

Labarai masu alaka