'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi 9

chad boko haram Hakkin mallakar hoto AFP/getty
Image caption Wasu daga cikin sojojin Chadi masu yaki da Boko Haram

Rahotanni daga N'djamena na kasar Chadi sun ce wasu 'yan bindiga da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun halaka sojojin Chadin tara, yayin wani hari.

Rahotannin sun ce 'yan bindigan sun kai harin ne a wani sansanin sojin Chadin da ke Kaiga a arewacin kasar, kusa da tabkin Chadi.

Wani kakakin sojin Chadi, Kanal Azem Bermandoua ya ce tara daga cikin sojojin kasar sun mutu, sannan wasu ashirin da takwas sun jikkata.

Kakakin ya kara da cewa, su ma sojojin sun kashe mayakan kungiyar ta Boko Haram 28 a arangamar da suka yi.

Yankin da mayakan Boko Haram din suka kai harin, dake kusa da iyakar Nijar, ya kasance wani wuri da mayakan kungiyar suka dade suna kai ma farmaki.

Wani hari makamancin wannan da 'yan bindigan suka kai a a watan Satumba a yankin na Kaiga, ya yi sanadiyar mutuwar kimanin sojojin Chadin 4, yayin da aka kashe mayakan kungiyar da dama.

Garuruwa da kauyuka dake kan iyakokin Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar, sun ta fuskantar hare-hare daga kungiyar ta Boko Haram tun daga 2009.

A shekaru biyin da suka gabata, sojoji sun kori mayakan Boko Haram din a garuruwan da suka mamaye a Najeriya a 2014, sai dai duk da karya lagonsu da aka yi, suna ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake.