Yadda tattalin arziki zai taka rawa a zaɓen Iran

Iran election Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Many ordinary Iranians have not yet felt the benefits of sanctions relief

Yayin da ranar zabe a Iran ke kara karatowa, halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ya kasance babban lamari da 'yan takarar shugaban kasar shida suka mayar da hankali a kai.

Ganin yadda matsalar rashin aikin yi ta yi yawa sosai, wasu 'yan takarar suna alkawarin samar wa mutane guraben aikin yi, wasu kuma suna raba wa mutane kudi ne domin su ja ra'ayinsu.

Ga shugaban kasar Hassan Rouhani, yin nasara a zaben abu ne mai sauki a wurin shi saboda abubuwan da ya yi, sai dai kuma babu tabbas a sake zabensa.

Mista Rouhani ya yi kokarin cimma wata yarjejeniya da manyan kasashen yamma a 2015 game da shirin Iran na nukiliya mai cike da takaddama, inda ya kawo karshen rashin jituwa na tsawon lokaci da kasashen yamma.

An cire wa kasar takunkumin kasa da kasa da a ka sanya mata, sai dai kuma da dama daga cikin 'yan kasar ta Iran sun ce ba sa jin tasirin yaye takunkumin a rayuwarsu ta yau da kullum.

"A shekaru biyun da suka wuce, mutane da dama sun kauracewa kasuwar hada-hadar gidaje, suna fatan ko farashi zai sauka bayan an cire takunkumi, da kuma fargabar mai zai faru bayan zabe," in ji Ali Saeedi mai hada-hadar gidaje.

"Abokan aiki na da dama sun bar sun bar sana'o'insu saboda kasuwar ta mutu." Mista Saeedi ya kara da cewa.

Hukumar bayar da Lamuni ta Duniya, IMF ta ce bangaren hada-hadar gidaje a Iran ya yi kasa da kashi 13 cikin dari zuwa watan Maris na 2017, yayin da kuma tattalin arzikin kasar baki daya ya bunkasa da kusan kashi 6.6 cikin dari.

An samu akasarin ci gaban ne daga mai da kasar ta rika fitar wa kasuwannin duniya bayan an janye takunkumin da aka sanya mata.

Ire-iren alkawuran da ake ma jama'a

A wurin matasan Iran kamar Ali Saeedi, suna shan alkawura a 'yan kwanakin nan.

Magajin garin Tehran Mohammad Baqer Qalibaf, wanda ke takarar shugabancin kasar, ya ce zai samar da ayyukan yi miliyan biyar a shekaru hudu idan aka zabe shi.

Mafi kololuwar adadin guraben ayyukan yi da Iran da rika samarwa a cikin shekaru arba'in da suka wuce shi ne dubu dari shida a kowacce shekara.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An yi alkawuran bai wa matasa aikin yi

Matsalar rashin aikin yi a Iran a halin yanzu ya kai kashi 12.7 cikin dari, inda aka samu karin kashi 1.7 cikin dari daga bara.

Hakan na nufin adadin mutanen da basu da aikin yi a kasar ya kai miliyan uku da dubu dari uku.

Mutun guda a cikin uku na matasa 'yan tsakanin shekaru 15 zuwa 24 bai da aikin yi. Haka ma ko wacce mace mai tsakanin wadannan shekarun ba ta da aikin yi.

Ga wadanda basu da aikin yi, Mista Qalibah ya yi alkawarin ba su dala sittin da shida a kowanne wata, a karon farko cikin shekaru talatin da takwas tun bayan juyin juya halin kasar.

Neman kuri'u

Ebrahim Raisi, wani dan takarar mai ra'ayin gargajiya, ya shiga gaban Mista Qalibah wajen alkawari, inda ya ce zai samar da guraben ayyukan yi miliyan shida.

Mista Raisi mai shekaru 57, malami kuma tsohon mai shigar da kara, wanda ke tafiyar da wurin ibada na 'yan Shi'a dake birnin Mashhad, ya kuma yi alkawurin rubanya kudin da ake ba talakawa sau uku.

A zaman wata sakayya ta cire tallafin mai, ana biyan 'yan kasar ta Iran riyal dubu 455 a kowanne wata. Rubanya kudin sau uku ga talakawa miliyan ashirin da hudu a kasar, ya sa kudin zai kama dala biliyan uku da miliyan dari biyar kenan a shekara.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matsalar rashin aikin yi na karuwa a Iran

Mista Raisi bai fadi ko daga ina yake sa ran samun kudin ba.

"Abin kamar suna yin tayin kayan da aka yi gwanjonsu ne. Ba haka tattalin arzikin yake gudana ba," in ji Ahmad Alavi, wani dan kasar Iran masanin tattalin arziki da ke zaune a Stockholm na Sweden.

Ya kara da cewa "Wadannan kalamai ne masu dadin ji, amma abin da 'yan takarar suka manta shi ne, har yanzu ba a mance da abin da tsohon shugaba Ahmadinejad ya yi ba".

A lokacin mulkin toshon shugaban kasar Ahmadinejad daga shekarar 2005 zuwa 2013, ya fara rabawa mutane kudi yayin da yake cire tallafin mai, ya kuma rika bayar da bashin kudi marasa kudin ruwa mai yawa ga kananan 'yan kasuwa, sannan ya kaddamar da babban shirin bada gidaje ga talakawa.

Amma bayan Ahmadinejad ya sauka daga mulki, tattalin arzikin kasar ya komade da kashi 7 cikin dari a shekara, sannan aka samu hauhawar farashin kayayyaki da kashi 40 cikin dari.

Ya dora alhakin hakan akan takunkumin kasa da kasa da aka sanya wa kasar, sai dai masana tattalin arziki sun dora laifi ne akan manufofinsa da rashin alkinta tattalin arzikin.

Yin nasara a karo na biyu?

Shugaba Rouhani ya farfado da tattalin arzikin, tare da rage hauhawar farashin kaya.

Sai dai akwai fata da yawa akan shugaba Rouhani, kuma shi ma yana da laifi, ganin irin alkawuran kyautata rayuwa da yayi wa jama'a da zarar an cirewa kasar takunkumi.

Da dama daga cikin 'yan kasuwa masu zaman kansu a kasar sun ce za su ba shugaban Rouhani dama ta biyu.

"Muna so ya bunkasa yanayin gudanar da kasuwanci, ya kuma fito da tattalin arzikinmu daga tasku, da cin hanci da rashawa," in ji Hamid Hosseini, shugaban matatar mai ta Soroosh ta Iran.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hassan Rouhani ya tsaya takara a karo na biyu

Mista Hosseini, mamba ne a hukumar ciniki da masana'antu ta Iran, kuma shi ne ya kafa kungiyar masu safarar mai zuwa kasashen waje ta Iran.

Ya ce shugabannin kamfanoni masu zaman kansu sun hada kai cewa za su marawa shugaba Rouhani baya.

Sai dai wasu matasa a Iran din irin su Ali Saeedi, ba su yanke shawara akan ko wa za su zaba ba.

Ya ce "Abin da na damu da shi kawai shi ne kasuwar hada-hadar gidaje ta farfado. Manyan 'yan takarar dai sunce Hassan Rouhani, da Ebrahim Raisi da kuma Mohammed Baqer Qalibaf."