Boko Haram ta sako 'yan matan Chibok '82'

Chibok
Image caption Boko Haram ta taba cewa ta musuluntar da 'yan matan wadanda mafi yawansu Kiristoci ne

Kungiyar Boko Haram ta sako 'yan mata 82 daga cikin 'yan makarantar Chibok kusan 200 da ta sace shekaru uku da suka wuce.

Sakin 'yan matan ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin mayakan da gwamnati wacce kungiyar agaji ta Red Cross da wasu kasashe suka shiga tsakani.

Wani soja da bai amince a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC cewa an sako 'yan matan ne ta garin Banki da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.

"Mun karbi 'yan matan Chibok 82 wadanda 'yan Boko Haram suka saki, kuma suna hannunmu," a cewar sojan.

Kawo yanzu hukumomi ba su tabbatar da labarinba a hukumance, amma kuma ba su musanta ba.

Babu cikakken bayani kan yarjejeniyar da aka cimma, wacce aka shafe watanni ana kulla wa. Kuma babu tabbas ko an biya kudin fansa.

Shekara uku kenan da mayakan Boko Haram suka sace daliban fiye da 200 daga makarantarsu da ke garin Chibok.

A watan Oktoban bara ne aka sako wasu 'yan matan 21 bayan makamanciyar wannan tattaunawar.

An kubutar da wasu guda biyu kuma a wasu lokutan na daban.

Yadda aka karbo 'yan matan

Wata majiya mai kusanci da yadda yarjejeniyar ta faru ta shaida wa BBC:

An ga wasu motocin Majalisar Dinkin Duniya guda hudu sun shiga jeji a kusa da garin Banki da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru.

Jiragen yaki biyu da kuma sojoji ta kasa ne suka yi musu rakiya. Kuma an ga wasu mutum biyu da fuskarsu a rufe.

Daga bisani ne za a wuce da 'yan matan da aka sako zuwa birnin Maiduguri, a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.

Sace 'yan matan Chibok a shekarar 2014 ya ja hankalin duniya sosai inda kaddamar da gagarumin kamfe na #BringBackOurGirls a shafukan sada zumunta domin ceto so.

Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin duk mai yi wu wa domin an ceto 'yan matan.

Sai dai wasu na zargin gwamnatin da biyan mayakan makudan kudade domin su sako 'yan makarantar, zargin da gwamnatin ta musanta a baya.