Faransawa na zaɓar shugabansu: Le Pen ko Macron

French Candidates Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai sassaucin ra'ayin goyon bayan 'yan kasuwa na fafatawa da mai tsaurin ra'ayin kishin ƙasa

Masu zaɓe a Faransa na ƙoƙarin fitar da gwani da zai zama shugaban ƙasar na gaba, bayan wani yaƙin neman zaɓe da ya raba kan ƙasar gida biyu.

Ana fafata zagaye na biyu ne tsakanin ɗan takara mai matsakaicin ra'ayi, Emmanuel Macron, ɗan shekara 39 kuma tsohon mai zuba jari a harkokin banki, da kuma mai tsaurin ra'ayin kishin ƙasa Marine Le Pen, 'yar shekara 48.

Faransawa a wasu ƙasashen da kuma 'yan ƙasar da ke ƙetare sun fara kaɗa ƙuri'unsu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zaɓe a wasu ƙasashen ƙetare kamar Guiana ta Faransa suna kaɗa ƙuri'unsu

Rumfunan zaɓe za su buɗe a babban birnin ƙasar da ƙarfe 08:00 na safe agogon Faransa daidai da ƙarfe 06:00 agogon GMT a ranar Lahadi sannan a kammala zaɓe da ƙarfe 07:00 na yamma daidai ƙarfe 05:00 GMT.

A wasu manyan birane tashoshin zaɓe za su ci gaba da kasancewa buɗe har zuwa ƙarfe 08:00 na dare agogon Faransa, inda bayanai ke cewa za a sanar da sakamako nan take bayan rufe tashoshin.

A cikin watan jiya, masu zaɓe suka fitar da yan takara na manyan jam'iyyun gurguzu da Republican, abin da ya 'yan takara biyu suka rage.

A Lahadin nan kuma, za su fitar da ɗan takara guda tsakanin mai matsakaicin ra'ayi Emmanuel Macron da jagorar masu tsaurin ra'ayin kare ƙasa, Marine Le Pen.

Yayin da aka kawo ?arshen yaƙin neman zaɓe a ranar Juma'a, Mr. Macron ya fuskanci kutsen intanet.

Wani Bafaranshe ya ce:"Ban yi mamaki ba, mun san cewa akwai ƙasashen waje masu son yin katsalandan cikin wannan zaɓe na shugaban ƙasa a Faransa.

Kuma ga shi sai da abu ya zo Ƙarshe kafin fara kaɗa ƙuri'a."

Dokokin zaɓen Faransa sun haramta wa 'yan takara wani jawabi ga jama'a a wannan lokaci.

Sai dai shugaban Faransa mai barin gado, Farancois Hollande ya ce al'amarin ba zai tafi haka nan ba.

Labarai masu alaka