Buhari ya sake tafiya London domin jinya

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A farkon shekarar nan ne Shugaba Buhari ya shafe kusan wata biyu yana jinya a London.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake komawa Ingila domin likitoci su duba lafiyarsa.

Sanarwar da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar, ta ce shugaban zai gana da likitocin ne a wani bangare na ci gaba da jinyar daya je a watannin baya.

Sai dai ya ce babu tabbacin ranar da shugaban zai dawo domin likitoci ne kawai za su fayyace hakan.

Amma ya ce ka da 'yan kasar "su tayar da hankulansu domin babu wani abin damuwa".

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da mulkin kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Kuma tuni shugaban ya "aika wasika ga majaisar dattawa" domin sanar da su cewa Osinbajo ne zai ci gaba da lura da al'amura.

A watan Fabrairu ne Shugaba Buhari ya shafe kusan wata biyu yana jinya a London.

Femi Adesina ya kara da cewa shugaban ya jinkirta tafiyar tasa ne domin ya gana da 'yan matan Chibok 82 da Boko Haram ta saki.

Shugaban ya yaba wa 'yan kasar game da irin addu'o'in da suke yi masa.

A makon da ya gabata ne wasu 'yan kungiyar farar hula suka yi kira ga shugaban da ya koma asibiti saboda ya kula da lafiyarsa.