Ba zan daina ficewa daga fili ba kan wariyar launin fata - Sulley Muntari

Sulley Muntari

Sulley Muntari
Image caption Sulley Muntari ya bukaci duk dan wasan da aka nuna wa wariyar launin fata da ya ta shi ya yaki lamarin

Dan wasan tsakiya na Ghana Sulley Muntari ya ce ko a yanzu zai sake ficewa daga fili, kuma ba zai daina hakan ba, in dai aka ci zarafinsa ta wariyar launi, yana mai zargin Fifa da Uefa da kin daukar matakin da ya kamata a kan ta'adar a wasan kwallon kafa.

Alkalin wasa ya kori dan wasan mai shekara 32, na Ghana wanda yake a kungiyar Pescara ta Italiya, bayan da ya fice daga fili, bisa zargin cewa ana cin mutuncinsa ta wariyar launin fata a lokacin wani wasan gasar Serie A ta Italiya.

A wata hira da ya yi da BBC, tsohon dan wasan na Portsmouth, ya ce wannan ta'ada ta wariyar launin fata, tana nan a ko ina, kuma karuwa take yi matuka, yana mai kira ga 'yan wasa da su rika kaurace wa wasa domin a kawo karshenta.

Muntarin ya ce, shi kam ya ga kwal, domin an dauke shi ne kamar wani mai mugun laifi.

Ya ce ya fice ne daga fili a lokacin da ake cin mutuncin nasa, saboda yana ganin bai dace ba ya ci gaba da kasancewa a filin yayin da ake muzanta shi.

Da farko dai an haramta wa Muntarin wasa daya ne bayan da ya nemi alkalin wasa Daniele Minelli ya dakatar da wasan da suke yi da Cagliari ranar 30 ga watan Afrilu.

Amma maimakon alkalin wasan ya saurare shi, sai ma ya ba shi katin gargadi a minti na 89, lamarin da ya harzuka tsohon dan wasan na Ghana ya fice daga fili, kan hakan ne kuma alkalin wasan ya kara masa kati na biyu.

Hukumar kwallon kafa ta Italiya ta soke hukuncin hana shi wasa daya, bayan da ta ce ta yi nazari kan lamarin nasa.

Haka shi ma dan wasan baya na Juventus dan kasar Morocco Medhi Benatia, ya katse wata hira ta bayan wasa da ake yi da shi a talabijin ranar Lahadi, bayan da ya ce, ya ji wani cin mutunci na wariyar launi da aka yi masa, a abin jin magana da ya sanya a kunnensa (earpiece).