Burinmu mu fafata da Buhari a 2019 — PDP

PDP ta ce ba ta maraba da neman shugaba Buhari ya yi murabus
Image caption PDP ta ce ba ta maraba da neman shugaba Buhari ya yi murabus

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta PDP ta ce babban burinta shi ne ta sake fafata wa da shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019.

Jam'iyyar ta PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi, ta ce ba ta goyon bayan kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar ke yi na neman shugaban ya yi murabus domin ya fuskanci jiyyar rashin lafiyarsa.

Sanata Ahmed Makarfi, ya shaida wa BBC cewa, PDP ba ta maraba da yin murabus din shugaba Buhari domin ta fi son idan lokacin zaben 2019 ya zo a nuna 'yar kashi.

A cewarsa, jam'iyyar PDP na sahun gaba wajen bai wa shugaba Muhammadu Buhari shawarar ya sake koma wa Ingila domin duba lafiyarsa, kuma matakin da ya dauka yanzu ya nuna cewa shugaban ya yi amfani da wannan shawara.

Shugaban jam'iyyar ya kuma ce suna yi wa shugaba Buhari fatan samun lafiya, inda ya zargi gwamnatin APC mai mulki da boye gaskiyar halin rashin lafiyar shugaban kasar tun da farko.

Sanata Ahmed Makarfi, ya ce jinkirin da aka rika yi na komawar shugaba Buhari asibiti ka iya janyo tabarbarewar rashin lafiyar shugaban kasar.

Labarai masu alaka