Indonesia: Gwamna da ya yi saɓo zai sha ɗauri

Ana zargin mr Purnama da cin mutuncin musulmai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin mr Purnama da cin mutuncin musulmai

An yakewa Gwamnan birnin Jakarta, babban birnin Indonesia mai bari gado hukuncin daurin shekar biyu a gidan kaso bayan da aka same shi da laifin aikata sabo da kuma tanzura jama'a don su tayar da hankali.

Basuki Tjahaja Purnama, wanda ake wa lakabi da suna Ahok, shi ne kabila kuma Kirista na farko da ya taba zama gwamna a birnin.

Wasu dai na kallon shari'ar da ake yi masa a matsayin zakaran gwajin dafi ga mutunta mabiya sauran addinai a kasar.

An dai tuhumi Mr Purnama ne da cin mutuncin Musulmai saboda yadda ya rika kawo misalai da wasu ayoyin alkur'ani a lokacin yakin neman zabe.

Mr Purnama dai ya musanta cewa ya aikata sabo kuma ya ce zai daukaka kara a kan hukuncin.

Kalaman da Mr Purnama ya yi game da Musulunci dai sun janyo kakkausar suka, inda wasu Malaman addinin Musulunci suka rika gudanar da gangami suna neman a tuhume shi, yayin da wasu masu tsattsauran ra'ayi ma suka rika cewa ya kamata a yanke masa hukuncin kisa.

Labarai masu alaka