An rantsar da sabon shugaban Koriya ta Kudu

Mr Moon ya ce a shirye yake ya je Koriya ta Arewa matukar yanayin da ake ciki ya inganta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mr Moon ya ce a shirye yake ya je Koriya ta Arewa matukar yanayin da ake ciki ya inganta

An rantsar da sabon shugaban kasar Koriya ta Kudu, Moon Jae-in, bayan da ya samu nasara a zaben da aka yi.

Ana kyautata zaton nan gaba kadan Mr Moon, wanda lauya ne da ke fafutukar kare hakkin bil dama, zai sanar da wadanda zai nada a akan manyan mukaman kasar.

Rahotanni sun ce Mr Moon ya kuduri aniyar dawo da martabar kasar daga rudanin da ta shiga har ta kai an tsige tsohuwar shugabar kasar, Park Geun-hye.

Bukin rantsar da sabon shugaban kasar an yi shi ne ba tare da tara dimbim jama'a inda aka shafe mintuna goma kacal wajen rantsuwar.

Gabanin rantsar da shi dai, sabon shugaban kasar ya shaida wa al'ummar Koriya ta Kudu cewa, yana son ganin kowa yana tafiyar da al'amuran sa a kasar ba tare da tsangwama ba.

Dangane da batun dangantakar kasar da Koriya ta Arewa kuwa, sabon shugaban ya ce a shirye yake yaje kasar matukar yanayin da ake ciki ya inganta, inda ya ce yana fatan nan gaba zai gana da shugaban Amurka Donald Trump ma.

Labarai masu alaka