Amurka: Shugaban FBI ya ce ba ya nadamar korarsa da aka yi

James Comey ya ce ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa game da korar da aka yi masa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption James Comey ya ce ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa game da korar da aka yi masa

Shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka,FBI da Donald Trump ya kora ya mayar da martani a kan korar sa da aka yi a cikin wata wasika da ya aikewa hukumomin gwamnati da ma yan uwa da abokan arziki.

James Comey, ya ce ba zai wani ba ta lokaci a kan matakin korar ta sa ba, ko kuma yadda aka yi aka aiwatar da korar ta sa.

Ya ce, ya jima da sanin cewa shugaban kasa na iya korar shugaban hukumar ta FBI a kan kowanne dalili, koma rashin dalili.

Mr Comey ya kara da cewa,a lokacin rikici, yakamata Amurkawa su dauki hukumar ta FBI a matsayin abar dogaro da gaskiya da kuma yanci.

A ranar Talatar da ta gabata ne, shugaban Donald Trump ya kori shugaban hukumar ta FBI.

Fadar gwamnatin Amurkan, ta ce, Mr Trump ya ce ana bukatar sabon shugabanci a hukumar domin mai do mata da amincin da jama'a su ke da shi a kan hukumar ta FBI .

An samu suka daga bangarori daban-daban game da korar shugaban hukumar ta FBI.

An dai mikawa Mr Comey takardar sallamar ne a lokacin da ya ke yiwa ma'aikatan hukumar jawabi a Los Angeles.

Mr Comey dai na jagorantar wani bincike da ke da alaka da kwamitin yakin neman zaben Mr Trump da kuma Rasha.

Labarai masu alaka