Nigeria: 'Mun sayo jiragen yaki 14'

Najeriya za ta sayi jiragen yaki samfurin Embraer A-29 Super Tucano kan kudi dala miliyan 600 daga Amurka Hakkin mallakar hoto NAF
Image caption Najeriya za ta sayi jiragen yaki samfurin Embraer A-29 Super Tucano kan kudi dala miliyan 600 daga Amurka

Gwamnatin Nigeria ta ce ta sayo jiragen yaki kimanin 14 a kokarinta na karfafa guiwar rundunonin sojin kasar wajen tunkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba zata sayo karin wasu jiragen yakin daga Amurka domin taimaka wa dakarun sojin kasar wajen murkushe kungiyar Boko Haram.

A halin yanzu dai an gayyaci ministan tsaron Najeriyar zuwa Amurka domin yi wa 'yan majalisar dokokin Amurka bayani kan batun sayen jiragen yakin da kasar ke nema daga Amurkar bayan da a watan jiya gwamnatin Trump ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen yakin.

Najeriya dai ta shafe shekaru tana fafutikar sayo jiragen yakin daga Amurkar amma gwamnatin Barack Obama ta ki amince wa da bukatar saboda fargabar da ta nuna ta yiwuwar a yi amfani da su wajen keta hakkin bil'adama.

Sai dai a wata hira da BBC, ministan tsaron Najeriya Mansur Muhammad Dan-Ali, ya ce nan bada jima wa ba ne zai ziyarci Amurkar don tattauna batun sayen jiragen yakin da zarar ya samu amincewar shugaba Muhammadu Buhari game da ziyarar.

Gwamnatin Najeriya ta sha cewa yakin da take yi da Boko Haram yana fuskantar cikas daga tanade-tanaden dokokin Amurka.

Tun a watan Fabrairu ne Shugaba Trump da takwararsa Muhammadu Buhari suka tattauna batun sayar da makaman a wata tattaunawa ta waya da suka yi.