An kai gagarumin farmakin intanet a ƙasashe 99

Hukumomin lafiya na Ingila da Scotland na cikin wadanda wannan hari na kwamfyutoci ya shafa. Hakkin mallakar hoto WEBROOT
Image caption Hukumomin lafiya na Ingila da Scotland na cikin wadanda wannan hari na kwamfyutoci ya shafa.

Wani gagarumin farmakin intanet ya auka kan hukumomi da kamfanoni a faɗin duniya.

Maharan sun yi amfani da wata manhaja da aka yi imani hukumar tsaron ƙasa ta Amurka ta ƙirƙira.

Wani tsari na kulle kwamfyutoci a wurare dubbai, inda yake neman sai an biya dala 300 na Bitcoin kafin buɗe su.

Harin ya illata kwamfyutocin Hukumar kula da lafiya ta ƙasar Burtaniya, kuma an samu rahotannin wasu ƙwayoyin virus da suka fantsama a kwamfyutocin ƙasashe irinsu Amurka da China da Rasha da Spaniya da Italiya da Taiwan.

Wani kamfanin tsaon intanet Avast ya ce ya ga rahotannin ƙwayoyin virus 75,000 da suka kama kwamfyutocin ƙasashe daban-daban.

Hukumomin lafiya na Ingila da Scotland na cikin wadanda wannan hari na kwamfyutoci ya shafa.

Hukumar tsaro ta tarayyar turai, Europol, ta ce ba a taba kai hari kan kwamfyutoci kamar wannan karon ba.

A watan jiya ne wasu masu kutsen kwamfyuta da aka sani da suna The Shadow Brokers suka yi iƙirarin sace manhajojin hukumar tsaron ƙasa ta Amurka.

Labarai masu alaka