Korea ta Arewa ta sake gwajin makamin da ya harzuƙa Amurka

Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan jiya ne Korea ta Arewar ta yi bikin nunin kayan yakinta a Pyongyang l

Amurka ta buƙaci a sake sanya takunkumi ga kasar Koriya ta Arewa, bayan ta sake gwajin makami mai linzami.

Fadar White House ta ce mahukuntan birnin Pyongyang ta daɗe da kasancewa mai taurin kai.

Sabon shigaban Korea da Kudu Moon Jae-in - wanda ke son bin hanyar lumana wajen tunkarar Koriya da Arewa -- ya danganta sabon gwaji a matsayin takalar fada da gangan.

Shi ma Fira ministan Japan Shinzo Abe, ya ce maimaita gwajin makamai masu linzamin, wata babbar barazana ce ga Japan.

Koriya ta Arewa ta yi sabon gwajin makamai masu linzamin ne a kusa da birnin Kusong, da ke arewa maso yammacin Pyomyang babban birnin kasar.

A baya ma, ta yi gwaje-gwajen makamai masu linzami da dama, abin da ya janyoikakkausar suka daga kasashen duniya, da kuma kara haifar da tankiya tsakaninta da Amurka.

A watan da ya gabata ne gwajin makamai masu linzami biyu da Pyonyang din ta yi duka suka gamu da cikas, bayan da rokokin suka tarwatse mintoci kadan bayan harba su.

Image caption Sojojin Koriya ta Arewa sun yi fareti da baje kolin makamai

Rundunar sojin Korea ta Kudu ta ce an harba wani makamin da ba ta iya tantance ko wanne iri ba ne daga birnin Kusong, amma ba ta yi karin bayani ba.

An ba da rahoton cewa Korea da Arewar na da ƙarfin ƙera makaman nukiliya da za a iya ɗaura su a kan manyan makamai masu linzmin masu cin dogon zango da nisansu ka iya kai wa Amurka.

Amurkar ta zargi sauran mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kin karfafa takunkumi kan Korea ta Arewar, inda ta yi kira ga musammam China ta yi amfani da karfin cinikayyar da take da shi.

Amma kuma duk da tsamin da dangantarsu ta yi, Korea ta Arewar a baya bayan nan ta ce za ta yi wata tattaunawa da Amurka muddin aka sanya sharudda masu ma'ana.

Kalaman sun fito ne daga babban jami'in diplomasiyya na Korea ta Arewar, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi farin cikin haduwa da shugaba Kim Jong-un.

Labarai masu alaka