Ranar farko ta mulkin matashin shugaban Faransa

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Emmanuel Macron za kasance shugaban Faransa mafi karancin shekaru tun bayan Napoleon

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron, zai saɓa rantsuwar kama aiki mako guda bayan gagarumar nasarar da ya samu a kan abokiyar fafatawarsa mai tsaurin ra'ayin kishin ƙasa, Marine Le Pen. Mista

Macron mai sassaucin ra'ayi da ke goyon bayan haɗin kan Turai ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arziƙin Faransa da yi wa tsohon tsarin siyasar ƙasar garambawul.

Sai dai, akwai buƙatar sabuwar jam'iyyarsa Republican on the Move ta ci kujeru da yawa na majalisar dokoki a zaɓen da za a yi cikin watan gobe don cim ma burukansa.

An tanadi tsattsauran matakin tsaro a faɗin birnin Paris don ƙaddamar da Emmanuel Macron a ranar Lahadin nan.

Ɗan takarar mai zaman kansa, Mista Macron ya samu gagarumar nasara a zaɓen da aka yi zagaye na biyu a ƙarshen makon jiya.

Tsohon mai zuba jarin cikin harkokin banki, bai taɓa tsayawa wata takara a wani zaɓe kafin wannan ba, kuma a bara ne kawai ya kafa tafiyar siyasarsa ta masu sassaucin ra'ayin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jerin motoci da tutocin kasar Faransa a kofar fadar Elysees yayin da ake shirin rantsar da Mr Macron

Emmanuel Macron ɗan shekara 39, zai karɓi mulki daga shugaba Francois Hollande.

An sanya ƙarin ɗaruruwan 'yan sanda don gudanar da sintiri a lokacin gudanar da bikin rantsuwar a fadar shugaban ƙasa ta Elysee.

Faransa na ƙarƙashin dokar-ta-ɓaci tun bayan kai hare-haren ta'addanci a shekara ta 2015, don haka za a rufe mafi akasarin sassan tsakiyar birnin Paris ga masu ababen hawa a duk tsawon safiya.

Bayan karɓar mulki, sabon shugaban Faransar zai duba faretin dakarun sojin ƙasar, kafin a harba masa bindigar ban girma sau 21.

Labarai masu alaka