"Ka karya azumi, ka tafi gidan yari"

Pakistan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Musulmai a Pakistan lokacin azumi a 2014

Kwamitin harkokin addini na majalisar dattijan Pakistan ya amince da yi wa wata doka gyara, wacce za ta tanadi hukunci mai tsanani a kan duk wanda aka kama ya karya azumi a watan Ramadana dake tafe.

Dokar za ta tanadi cin tara mai yawa da kuma daurin wata uku a gidan kaso ga Musulmin da aka samu yana shan taba ko cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin Ramadana.

Shekaru talatin da hudu kenan da Pakistan ta kafa dokar hana Musulmai cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin Ramadana, amma a wannan karo, hukumomi a kasar na so su kara tsananta hukuncin karya azumi.

Sai dai wata daga cikin 'yan siyasa masu fada a ji a Pakistan, Bakhtawar Bhutto-Zardari ta soki yunkurin tsananta hukuncin.

Bakhtawar Bhutto-Zardari, babbar 'yar tsohuwar Firayiministar kasar, Benazir Bhutto, ta bayyana matakin a matsayin mai daure kai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lokacin bude baki a watan Ramadan a Pakistan a 2014

A wani rubutu da tayi a shafinta na twitter, Bhutto-Zardari, ta yi shagube, inda ta ce hakan na nufin za a kama yara da tsofaffi da marasa lafiya idan suka kwankwadi ruwa kenan?

Ta ce wasu mutane a kasar zasu mutu saboda kishin ruwa da zafi, idan aka tilasta musu kame baki.

Kalaman na ta dai sun sa mutane a kasar na ta bayyana ra'ayoyinsu.

Majalisar dokokin kasar dai ba ta riga ta amince da dokar ba, amma masu sharhi sun ce akwai yiwuwar za ta amince da ita.