'Gazawar iyaye na janyo ƙaruwar fyaɗe a Kano'

Gwamnan Kano Ganduje
Image caption Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce matsalar ta zama ruwan dare

Wasu lauyoyi a Kano sun ce gazawar iyaye wajen fallasa mutanen da suka yi wa 'ya'yansu fyaɗe ta janyo ta'azzarar wannan matsala.

Rundunar 'yan sandan Kano ta ce daga farkon shekara ta 2017 zuwa watan Mayu, an samu rahoton aikata fyaɗe sama da 133.

A bara kuwa, irin wannan fyaɗe ya kai har 547, ciki har ƙananan yara maza da mata.

Shugaban ƙungiyar lauyoyi na Kano, kuma jagoran ƙungiyoyin kare haƙƙin mutanen da aka yi wa fyaɗe, Barista Ibrahim Mukhtar ya ce: "(Abin damuwa ne ganin yadda) matsaloli suke kifar da shari'o'in fyaɗe".

A cewarsa iyaye ba sa son zuwa su ba da shaida kan fyaɗen da aka aikatawa 'ya'yansu.

"Kai akwai shari'ar da na sani, da aka matsa musu sai sun zo sun ba da shaida. Sai (iyayen) suka tashi daga Kano suka koma Zaria.

Saboda kawai kar su zo gaban kotu su ba da shaida."

Da dama cikin masu aikata irin wannan fyaɗe a cewar 'yan sanda makusanta ne, yayin da wasu iyaye ke ɗari-ɗari game da gurfana a kotu don ba da shaida kan lalatar da aka yi da 'ya ko ɗansu.

Masanin shari'ar ya ce alƙali da shaida yake amfani, ba da labari ba.

Ya ce wata matsalar kuma game da shari'o'in fyaɗe a Nijeriya ita ce rashin ci gaba ta fannin aikin ɗakunan gwaje-gwajen kimiyya.

A cewar Barista Ibrahim Mukhtar, gaba ɗaya Nijeriya a waje guda ne ake yin gwajin tantance zanen halittun mutum (DNA) wanda ke da matuƙar tasiri a shari'ar fyaɗe.

Fyaɗen da aka yi wa wata jaririya 'yar wata takwas a baya-bayan nan, ya yi matuƙar tayar da hankula ba kawai a birnin Kano ba, har ma a Najeriya gaba ɗaya.

Ita dai rundunar 'yan sanda ta ce matsalar aikata fyaɗe ƙaruwa take yi maimakon raguwa.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin waɗanda aka yi wa fyaɗe a Kano, sun lashi takobin yaƙi da masu aikata wannan mummunar ɗabi'a musammam kan ƙananan yara.

Sai dai, a ra'ayin Barista Ibrahim Mukhtar duk ƙoƙarin da za su yi, sai iyayen yaran da aka yi wa fyaɗe sun riƙa fita suna ba da shaida, ta yadda doka za ta yi aikinta don hakan ya zama darasi ga sauran mutane.