Ɗakin kimiyyar da zai haɗa abokan gaba inuwa ɗaya

Dakin gwaje-gwajen kimiyya na Sesame a kasar Jordan Hakkin mallakar hoto KATE STEPHENS
Image caption Wannan wani nuna hadin kai ne na ba kasafai ba a tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya

Sarki Abdullah na Jordan na buɗe wani sabon ɗakin gwaje-gwajen kimiyya, wanda ake fata zai bunƙasa ayyukan bincike na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Tsawon shekara ashirin da ta gabata ne aka fara tunanin kafa katafaren ɗakin binciken, amma sai aka yi ta samun tangarɗa.

Wannan wani ƙoƙarin haɗa kai ne na ba-sabon-ba a tsakanin ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya, duk da zaman doya da man jan da ke tsakanin wasunsu.

Wasu ƙasashe da ke cikin shirin, ba su da hulɗar jakadanci da juna, wasu kuwa kamar Iran da Isra'ila ƙarara abokan gabar juna ne.

Ɗakin binciken ka iya nazarin komai, kama daga ƙwayoyin halittu masu cutar daji da takardun tarihi da aka rubuta shekaru aru-aru, shi ne dai irinsa na farko da zai yi aiki a Gabas ta Tsakiya.

Masu bincike da suka hada da Iraniyawa, da Palasdinawa da kuma Yahudawa- da ba su cika shan inuwa ɗaya da juna ba--yanzu za su rika aiki da wannan na'ura tare.

Rashin jituwa dai na ƙara ta'azzara a yankin Gabas ta Tsakiya, baya ga rikicin Syria da ke kusa da ƙasar ta Jordan wadda za ta jagoranci buɗe wannan cibiya.

Hakkin mallakar hoto KATE STEPHENS
Image caption Cibiyar bincken ta Sesame a kasar Jordan za ta kasance hanyar hadin kai ta farko yankin Gabas ta Tsakiya

Shi kansa Sarki Abdullah na II a watan da ya gabata, ya soki ƙasar Iran a baya-bayan nan kan rawar da take takawa a rikicin da ke faruwa a kasar Syria.

Labarai masu alaka