Nigeria: A wata na uku tashin farashi ya ja baya

Kasuwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sai dai wasu 'yan kasar na cewa ba su gani a kasa ba

A Najeriya kaifin tashin farashin kayayyaki ya ragu a wata na uku a jere a watan Afrilu, sakamakon raguwar da hauhawar farashin kayan abinci ta yi.

Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar ranar Talata sun nuna cewa farashin kayayyayi a watan na Afrilu ya tashi a kan kashi 17.24 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 17.26 cikin 100 a watan Maris.

Farashin kayayyaki ya kwashe kusan shekara guda yana tashin gwauron zabi a kasar har zuwa watan Janairun 2017, saboda faduwar farashin danyen man fetur, da karancin dalar Amurka, da wasu dalilai.

Hakan dai na nufin a karo na uku a jere, hauhawar farashin ba ta yi yawa kamra watannin da suka gabata ba.

Hauhawar farashi: 'Yan Nigeria na ɗanɗana kuɗarsu

'Halin da Nigeria ta shiga ya ƙara mana matsin rayuwa'

Ana zanga-zanga kan 'matsin tattalin arziki' a Nigeria

Sai dai kuma a birnin Kano na arewacin kasar, ra'ayoyin masu saye da 'yan kasuwa sun sha bamban game da sassaucin hauhawar farashin.

'Yan kasuwa dai na cewa ana samun rangwame, amma masu saye da dama sun ce ba su gani a kasa ba.

Ibrahim Isa ya tattaro mana ra'ayoyin mutane daga Kasuwar Singer a Kano:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan saukar farashi

Labarai masu alaka