Ba mu amince da kawancen Amurka da Kurdawa ba— Turkiyya

Shugabannin biyu sun tattauna akan yaki da ta'addanci a gabas ta tsakiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabannin biyu sun tattauna akan yaki da ta'addanci a gabas ta tsakiya

Mr Trump da shugaba Erdogan na Turkiyya sun gana a fadar White House ta Amurka, inda suka tattauna a kan aniyarsu ta yaki da ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya.

To sai dai, Turkiyya ta fito karara ta nuna adawarta ga kawancen Amurka da dakarun Kurdawa a Syria da ke yaki da kungiyar IS.

Kuma yayin da su ke wa 'yan jarida jawabi, Mr Erdogan ya nuna cewa Turkiyya baza ta taba amincewa da wannan hadin kan ba.

Turkiyya dai na daukar kungiyar Kurdawan masu fafutuka a Syria ta YPG a matsayin wani bangare na kungiyar Kurdawa ta PKK da ke tayar da kayar baya a kasar.

Labarai masu alaka