'Masu teba na iya kamuwa da shanyewar barin jiki'

Masu teba zasu iya kamuwa da hawan jini ko ciw Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu teba zasu iya kamuwa da hawan jini ko ciwon zuciya

Masana kimiyya a Birtaniya sun nuna shakku a kan bayanan da ke cewa wasu masu teba za su iya kasancewa suna da jiki da kuma lafiya.

Binciken da aka gudanar a baya sun nuna cewa a duk kaso daya cikin uku na masu teba suna da lafiya, kuma ba su da hawan jini da kuma yawan maiko a jikinsu.

To sai dai kuma masu bincike a jami'ar Birmingham sun gano cewa yawan maiko a jikin mutum na kara hadarin kamuwa da cutukan da suka shafi zuciya da shanyewar barin jiki.

An yi wannan binciken ne a kan mutane miliyan uku da rabi a cikin shekaru ashirin.