Fufu ko Sakwara na da matukar farin jini a Ghana

Ana hada fufu ko sakwara da miyoyi kala-kala Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana hada fufu ko sakwara da miyoyi kala-kala

Fufu ko kuma sakwara wani abincin nahiyar Afrika ne da ake dakawa.

Wannan nau'in Abinci, mutane na sha'awarsa a kasar Ghana.

Ana dai amfani da wannan nau'in abincin a lokutan bukukuwa da taruka, wani sa'in ma a kan dafa wannan abinci a gidaje domin aci.

Ana hada shi da miyoyi kala-kala, kamar miyar kwa-kwa da miyar gurjiya.

Masu sayar da abinci ma kan daka fufu domin sayarwa jama'a a kasar.

Ana hada wannan nau'in abinci ne da rogo da kuma bawon ayaba sai a nika daga nan kuma sai a dafa a kuma daka shi a turmi.

Al'ummar kasar Ghana dai na matukar sha'awar wannan nau'in abinci na fufu ko sakwara.

Labarai masu alaka